عَنْ أَبِي سَعِيدٍ رَضيَ اللهُ عنه:
أَنَّ جِبْرِيلَ أَتَى النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ اشْتَكَيْتَ؟ فَقَالَ: «نَعَمْ» قَالَ: «بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ، مِنْ كُلِّ شَيْءٍ يُؤْذِيكَ، مِنْ شَرِّ كُلِّ نَفْسٍ أَوْ عَيْنِ حَاسِدٍ، اللهُ يَشْفِيكَ بِاسْمِ اللهِ أَرْقِيكَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2186]
المزيــد ...
Daga Abu Sa'id - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa (Mala’ika) Jibril ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Ya Muhammad baka da lafiya ne? sai ya ce: «Eh» ya ce: «Da sunan Allah nake maka ruƙya, daga dukkan abinda zai cutar da kai, daga sharrin kowane rai ko maitar mai hassada, Allah Ya warkar da kai, da sunan Allah nake maka ruƙya».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2186]
Mala'ika Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya tambaye shi: Ya Muhammad kana fama da rashin lafiya ne? Sai ya ce: Eh. Sai Mala’ika Jibril ya yi wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi masa ruƙya da faɗinsa: «Da sunan Allah» ina mai neman taimakonSa «Nake maka ruƙya» nake nema maka tsari. «Daga dukkan abinda yake cutar da kai» ƙarami ne ko babba. «Daga kowace rai» mummuna. «Ko maitar mai hassada» da ya kai gareka, Allah «Ya warkar da kai» kuma ya kareka daga dukkanin cutuka. «Da sunan Allah nake maka ruƙya» ya maimaita shi ne dan kai matuƙa, kuma ya fara da shi kuma ya rufe da shi dan nuni zuwa ga cewa babu wani mai amfanarwa sai Shi - tsarki ya tabbatar maSa -.