عن عبد الله بن مسعود رضي الله عنه قال: سمعت رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«إنَّ الرُّقَى والتَمائِمَ والتِّوَلَةَ شِرْكٌ».
[صحيح] - [رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 3883]
المزيــد ...
Daga Abdullahi ɗan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbat a gare shi - yana cewa:
"Lallai cewa tawaida da layu da tiwala (tsafin juyar da tunani musamman tsakanin ma'aurata) shirka ne".
[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 3883]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana wasu abubuwa (waɗanda) aikatasu yana daga shirka; daga cikinsu akwai:
Na ɗaya: Tawaida: Zancen da 'yan Jahiliyya suke neman waraka da shi wanda ya haɗo shirka.
Na biyu: Layu na tsarkiya da makamancinta: Waɗanda ake ratayawa yara da dabbobi da wasunsu dan tunkuɗe kambun baka.
Na uku: Tiwala: Wacce akeyi don jawo soyayyar ɗaya daga cikin ma'aurata zuwa ɗayan.
Waɗannan al'amuran suna daga shirka; domin suna daga cikin riƙar abu a matsayin sababi, kuma shi ba sababi ne na shari'a ba wanda ya tabbata da dalili, ba kuma sababi ne na zahiri ba da ya tabbata da gwadawa. Amma sabubba na shari'a kamar karanta Al-ƙur'ani, ko na zahiri kamar magunguna da suka tabbata ta hanyar gwadawa, to, su sun halatta tare da ƙudire cewa su sabubba ne, kuma amfani da cuta suna hannun Allah ne.