عن عمرو بن شُعيب عن أبيه عن جدِّه قال: قال رسولُ الله صلى الله عليه وسلم:
«مُرُوا أولادكمِ بالصلاةِ وهم أبناءُ سبعِ سِنينَ، واضرِبوهم عليها وهم أبناءُ عَشرٍ، وفرِّقوا بينهم في المَضاجِعِ».
[حسن] - [رواه أبو داود] - [سنن أبي داود: 495]
المزيــد ...
Daga Amr Dan Shu'aib daga babansa daga kakansa ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"ku umarci 'ya'yanku da yin sallah alhali su suna 'yan shekara bakwai, kuma ku dake su akanta alhali su suna 'yan shekara goma, kuma ku raba tsakaninsu a wurin kwanciya".
[Hasan ne] - [Abu Daud Ya Rawaito shi] - [سنن أبي داود - 495]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa ya wajaba akan uba ya umarci 'ya'yansa - maza da mata - da yin sallah alhali suna da shekara bakwai, kuma ya sanar dasu abinda suke bukata dan tsaida ita. Idan suka kai shekara goma sai ya yi kari akan umarnin, sai ya yi duka akan kasa yin Sallar, kuma ya raba a tsakaninsu a shinfida.