+ -

عن عبد الله بن زيد بن عَاصِم المازِنِي رضي الله عنه قال: «خرج النبي صلى الله عليه وسلم يَسْتَسْقِي، فتَوَجَّه إلى القبلة يدْعو، وحَوَّل رِدَاءه، ثم صلَّى ركعتين، جَهَرَ فيهما بالقِراءة». وفي لفظ «إلى الْمُصَلَّى».
[صحيح] - [متفق عليه]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Zaid Dan Asim Almazini -Allah ya yarda da shi- ya ce: "Annabi ya futo ranci Aokon ruwa, sai ya fuskanci Alkibla yana Addua, kuma ya juya kayansa baibai, kuma yayi Sallah Rakaa biyu, kuma ya bayya karatu" a wani lafazin kuma "Zuwa Wurin Sallar Idi"
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

Bayani

Allah yana Jarrabar bayinsa da nau'o'i na Bala'i; don su rokeshi shi kadai kuma suyi ta ambatonsa, to yayain da akayi fari a lokacin Annabi ya futo filin Idi a sahara; don ya nemi shayarwa daga Allah, kuma wannan shine yake nuna kaskantar da kai ga Allah, sai ya fuskanci Alkibla, don fatan amsa Addua, kuma ya fara rokon Allah kuma yana neman agajinsa ga Musulmi, kuma ya gusar musu da abinda ya ke damunsu na fari, da kwadayin canza musu daga halin fari zuwa na Ni'ama, daga halin Matsuwa zuwa halin yalwa, sai ya juya gwadonsa izuwa daya bangaren, sannan kuma yayi musu Sallar Rokon ruwa raka'a biyu, kuma ya bayyana karatu a cikinsu; domin irinsu daya da Sallar Jumu'a.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Tagalog Kurdawa Portuguese
Manufofin Fassarorin