عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«لَوْ كَانَ لِابْنِ آدَمَ وَادِيَانِ مِنْ مَالٍ لَابْتَغَى وَادِيًا ثَالِثًا، وَلَا يَمْلَأُ جَوْفَ ابْنِ آدَمَ إِلَّا التُّرَابُ، وَيَتُوبُ اللهُ عَلَى مَنْ تَابَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1048]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Da a ce ɗan Adam yana da kwari biyu na dukiya da sai ya nemi wani kwarin na uku, babu abinda yake cika cikin ɗan Adam sai ƙasa, kuma Allah Yana karɓar tuban wanda ya tuba».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1048]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa da a ce ɗan Adam zai samu wani kwari cike da zinari, da zai so saboda kwaɗayinsa wanda shi ne ɗabi'arsa ta zama yana da wasu kwari biyun daban, kuma cewa shi ba zai gushe ba yana kwaɗayi akan duniya har sai ya mutu cikinsa ya cika da ƙasar ƙabarinsa.