+ -

عَنْ أبي سَعيدٍ الخُدريَّ رضي الله عنه قال: قال رسولُ الله صلَّى الله عليه وسلم ِ:
«إزْرَةُ المُسْلمِ إلى نصفِ السَّاق، وَلَا حَرَجَ -أو لا جُنَاحَ- فيما بينَهُ وبينَ الكعبينِ، وما كان أسفلَ منَ الكعبين فهو في النار، مَن جرَّ إزارَهُ بطرًا لم يَنْظُرِ اللهُ إليه».

[صحيح] - [رواه أبو داود وابن ماجه وأحمد] - [سنن أبي داود: 4093]
المزيــد ...

Daga Abu Sa'idul Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba".

[Ingantacce ne] - - [سنن أبي داود - 4093]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa mayafin (tufafin) namiji musulmi, shi ne dukkan abinda yake suturta rabin ƙwauri na ƙasa daga maza, halaye uku ne: Na farko: Abinda yake mustahabbi shi ne ya zama zuwa rabin ƙwauri. Na biyu: Wanda ya halatta ba tare da karhanci ba shi ne abinda ke ƙasansa (ƙwauri) zuwa idan sawu; sune ƙasusuwa biyu masu bayyana a mararrabar ƙwauri da diga-digi. Na uku: Wanda aka haramta shi ne ya zama ƙasa da idan sawu, kuma ana jiye masa tsoron kar wuta ta taɓa shi, idan kuma ya zama dan girman kai ne da nishaɗi da shisshigi to Allah ba zai yi duba zuwa gare shi ba.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Wannan siffar da kuma narkon ya keɓanci maza ne kawai, amma mata to antogance su daga hakan; domin cewa su an umarce su da suturta dukkan jikinsu.
  2. Dukkan abinda ke suturta rabin ƙasa daga maza to ana ce masa mayafi; kamar wando, da tufa da waninsu, kuma shi ya shiga cikin hukunce-hukunce na shari'a abin ambata a cikin wannan hadisin.