عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُ قَالَ:
«اللهُمَّ لَا عَيْشَ إِلَّا عَيْشُ الْآخِرَهْ، فَاغْفِرْ لِلْأَنْصَارِ وَالْمُهَاجِرَهْ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1805]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ya Allah babu wata rayuwa sai rayuwar lahira, ka gafartawa Mutanen Madina da waɗanda suka yi hijira».
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1805]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wata rayuwa ta haƙiƙa sai rayuwar lahira, a cikin yardar Allah da rahamarSa da kuma aljannarSa; domin rayuwar duniya mai gushewa ce, rayuwar lahira kuwa ita ce dawwamammiya mai wanzuwa, sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi addu'ar gafara da girmamawa da gyaruwa ga mutanen Madina waɗanda suka kawo ɗauki ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da Muhajirun, suka taimakesu, suka raba musu dukiyoyinsu, kuma (ya yi addu'a) ga Muhajirun waɗanda suka bar gidajensu da dukiyoyinsu suna neman falala daga Allah da kuma yarda.