+ -

عن أبي أمامة الباهلي رضي الله عنه قال: سمعتُ رسول الله صلى الله عليه وسلم يقول:
«اقرؤوا القرآنَ فإنَّه يأتي يوم القيامة شَفِيعًا لأصحابه، اقرؤوا الزَّهرَاوَين البقرةَ وسورةَ آل عِمران، فإنهما تأتِيان يوم القيامة كأنهما غَمَامَتان، أو كأنهما غَيَايَتانِ، أو كأنهما فِرْقانِ من طَيْر صَوافٍّ، تُحاجَّان عن أصحابهما، اقرؤوا سورة البقرة، فإن أخذها بَرَكة، وتركها حَسْرة، ولا تستطيعها البَطَلَة».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 804]
المزيــد ...

Daga Abu Umamah al-Bahili - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa:
«‌Ku karanta Alƙur’ani domin zai zo ranar alƙiyama yana mai ceton ma'abotansa, Ku karanta surori biyu Baƙara da al-Imran, domin cewa su za su zo a ranar alƙiyama kamar giza-gizai ko kamar wata tawagar tsuntsaye sun yi sahu, suna kare ma'abocinsu, ku karanta Surat al-Baƙara don haddace ta albarka ne, kuma barinta asara ne, kuma matsafa ba zasu iya ta ba».

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 804]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan dawwama kan karatun Alƙur'ani; domin shi (Alkur’ani) zai yi ceto a ranar alƙiyama ga masu karanta shi masu aiki da shi, sannan ya ƙarfafa karanta surori biyu: Baƙara da al-Imran, kuma ya ambace su da Zahrawani masu haske; saboda haskensu da kuma shiryarawarsu, kuma lallai ladan karanta su da tadabburin ma'anoninsu da kuma aiki da abinda ke cikinsu, zasu zo ranar alƙiyama kamar gizagizai biyu ko wasunsu, ko ka ce su garken tsntsaye ne waɗanda suka shinfiɗa fukafukansu sashinsu na saduwa da sashi, suna yi wa ma'abocinsu inuwa kuma suna kare shi. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ƙarfafa dawwama a kan karanta Suratul Baƙara da tadabburin ma'anoninta da kuma aiki da abinda ke cikinsu, kuma hakan a cikinsa akwai albarka da amfani mai girma a duniya da lahira, kuma barin hakan a cikinsa akwai asara da nadama a ranar alƙiyama, kuma daga cikin falalar wannan surar matsafa ba zasu iya cutar da wanda ya karantata ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Umarni da karanta alƙur'ani da kuma yawaita hakan, kuma shi (Alkur’ani) zai ceci ma'abotansa a ranar alƙiyama, masu karanta shi, masu riƙo da shiriyarsa, masu tsayawa kan abinda ya yi umarni da shi, masu barin abinda ya hana.
  2. Falalar karanta Suatul Baƙara da al-Imran da kuma girman ladansu.
  3. Falalar karanta Suratul Baƙara, kuma cewa ita tana kare ma'abocinta daga tsafi.
Fassara: Turanci urdu Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Kurdawa Portuguese Swahili Yaran Tailand Asami الأمهرية الدرية الرومانية المجرية الجورجية الخميرية الماراثية
Manufofin Fassarorin