عَنْ أَنَسٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
مِنَ السُّنَّةِ إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ فِي أَذَانِ الْفَجْرِ حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، قَالَ: الصَّلَاةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ.
[صحيح] - [رواه ابن خزيمة والدارقطني والبيهقي] - [صحيح ابن خزيمة: 386]
المزيــد ...
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce:
Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri).
[Ingantacce ne] - [Ibn Khuzaimah ya rawaito shi - Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi - Al-Dar Al-Kutni Ya Rawaito shi]
Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).