عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ:
«إنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي الخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ».
[قال النووي: حديث حسن] - [رواه ابن ماجه والبيهقي وغيرهما] - [الأربعون النووية: 39]
المزيــد ...
Daga ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Allah Ya gafarta wa al’ummata kurakurai da mantuwa da abin da aka tilasta su akansa».
[قال النووي: حديث حسن] - [رواه ابن ماجه والبيهقي وغيرهما] - [الأربعون النووية - 39]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Lallai Allah Ya yi wa al'ummarsa rangwame akan halaye uku: Na farko: Kuskure, shi ne abin da ya bijiro daga garesu ba tare da ganganci ba, kuma shi ne musulmi ya nufi wani abu da aikinsa sai aikin na sa ya dace da abin da bai yi nufi ba. Na biyu: Mantuwa, shi ne musulmi ya zama mai tina wani abu, saidai a lokacin aikata shi sai ya manta shi, to babu zunubi a kan hakan. Na uku: Tilastawa, za’a iya tilastawa bawa yin wani aikin da bai yi nufinsa ba tare da rashin ikonsa akan tunkuɗe tilastawar, a wannan lokacin zunubi ko ƙunci ba zai faɗa kansa ba. Tare da lura da cewa matashiyar hadisin a abin da ke tsakanin bawa da Ubangijinsa ne, a kan aikata abinda aka haramta, amma barin abin da aka yi umarni akan mantuwa to ba zai saraya ba, amma da ace wani laifi zai faru akan aikinsa to ba zai sarayar da wani haƙƙi na abin halitta ba, kamar yadda da ace zai yi kisa akan kuskure, ko ya lalata wata mota akan kuskure to wajibi ne ya biya.