عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«انْصُرْ أَخَاكَ ظَالِمًا أَوْ مَظْلُومًا». فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، أَنْصُرُهُ إِذَا كَانَ مَظْلُومًا، أَفَرَأَيْتَ إِذَا كَانَ ظَالِمًا كَيْفَ أَنْصُرُهُ؟ قَالَ: « تَحْجُزُهُ -أَوْ تَمْنَعُهُ- مِنَ الظُّلْمِ؛ فَإِنَّ ذَلِكَ نَصْرُهُ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6952]
المزيــد ...
Daga Anas ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
«Ka taimaki ɗan'uwanka azzalimi ko wanda aka zalinta».
Sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? ya ce: «Ka kare shi - ko ka hana shi - daga zalinci; domin cewa hakan taimakonsa ne».
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6952]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci musulmi da ya taimaki ɗan'uwansa musulmi, daidai ne ya kasance azzalimi ne ko wanda aka zalinta, sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, zan taimake shi idan ya kasance wanda aka zalinta ne, shi ne in hana a zalince shi, shin kana ganin idan ya zama azzalimi ta yaya zan taimake shi? Ya ce: Ka hana shi ka yi riƙo da hannunsa ka kare shi, ka hana shi zalincin; domin hakan shi ne taimakonsa akan Shaiɗaninsa da kuma ransa mai umartarsa da mummunan aiki.