+ -

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:
«إِنَّ اللهَ يَرْضَى لَكُمْ ثَلَاثًا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ ثَلَاثًا، فَيَرْضَى لَكُمْ: أَنْ تَعْبُدُوهُ، وَلَا تُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَأَنْ تَعْتَصِمُوا بِحَبْلِ اللهِ جَمِيعًا وَلَا تَفَرَّقُوا، وَيَكْرَهُ لَكُمْ: قِيلَ وَقَالَ، وَكَثْرَةَ السُّؤَالِ، وَإِضَاعَةِ الْمَالِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1715]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«‌Lallai Allah Ya yardar muku da abubuwa uku, kuma Yana ƙin abubuwa uku a gareku, Yana yardar muku: Ku bauta maSa, kada ku haɗa shi da wani abu a bauta, kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gabaɗaya kada ku rarraba. Kuma yana ƙi muku: Ƙila wa ƙala, da yawan roƙo, da kuma tozartar da dukiya».

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1715]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Yana son ɗabi'u uku daga bayinSa, kuma Yana ƙin abubuwa uku daga gare su, Yana so daga garesu: Su kaɗaita Shi da bauta kada su taranya wani abu a cikin bautarSa, kuma su yi riƙo da alƙawarin Allah da kuma Alƙur'ani da sunnar AnnabinSa bakiɗaya, kada su rarraba daga jama'ar musulmai. Kuma yana ƙi musu: zance mara anfani da yasasshiyar magana a cikin abinda babu ruwansu, da kuma tambayar abinda bai afku ba, ko roƙon mutane dukiyoyinsu, da kuma abinda ke hannunsu, da kuma abinda ba'a buƙatarsa, da tozarta dukiya da bada ita ba ta fuskar shari'a ba, da kuma bijiro da ita ga abinda zai lalata ta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Allah Yana son ikhlasi daga bayinSa a cikin bautarSa, kuma yana ƙin kafirci daga bayinsa.
  2. Kwaɗaitarwa akan riƙo da igiyar Allah - Maɗaukakin sarki -; saboda abinda ke cikinsa ha haɗuwar kai.
  3. Kwaɗaitarwa akan jama'a, da kuma umarni da lazimtarta da hada kai, da kuma hani daga kishiyarta na rarrabuwa da kuma saɓani.
  4. Hani daga yawan zancen da ba shi da amfani; domin idan ya kasance abin halattawa ne to a cikinsa akwai bata lokaci, idan kuma haramun ne to a cikinsa akwai yawan zunubi.
  5. Barin kutsawa a cikin labarun mutane da kuma bibiyar halayensu da kwaikwayar maganganunsu da kuma ayyukansu.
  6. Hani daga yawan roƙon dukiyoyin mutane.
  7. Haramta lalatar da dukiya, da kuma kwaɗaitarwa akan kiyayeta a abinda yake anfanarwa.
Fassara: Turanci Indonisiyanci Sinhalese Vietnam Swahili Asami الهولندية الغوجاراتية الرومانية المجرية الجورجية
Manufofin Fassarorin