عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«لَيْسَ الْوَاصِلُ بِالْمُكَافِئِ، وَلَكِنِ الْوَاصِلُ الَّذِي إِذَا قُطِعَتْ رَحِمُهُ وَصَلَهَا».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 5991]
المزيــد ...
Daga Abdullahi Dan Amr - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Mai sakayya bai zama mai sadarwa ba (sada zumunci), saidai mai asadarwa shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 5991]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari, Cewa cikakken mutum a sada zumunci da kuma kyautatawa 'yan uwa shi ne mutumin da yake fuskantar kyakkyawa da kyakkywa, Kai mai sadarwa a hakika a sada zumunci shi ne wanda idan an yanke zumuncinsa sai ya sadar da shi, idan sun munana masa to sai shi ya fuskantarsu da kyautatawa zuwa garesu.