عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ بَشِيرٍ رَضيَ اللهُ عنهُما قَالَ:
كُنْتُ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ رَجُلٌ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أُسْقِيَ الحَاجَّ، وَقَالَ آخَرُ: مَا أُبَالِي أَلَّا أَعْمَلَ عَمَلًا بَعْدَ الإِسْلَامِ إِلَّا أَنْ أَعْمُرَ المَسْجِدَ الحَرَامَ، وَقَالَ آخَرُ: الجِهَادُ فِي سَبِيلِ اللهِ أَفْضَلُ مِمَّا قُلْتُمْ، فَزَجَرَهُمْ عُمَرُ، وَقَالَ: لَا تَرْفَعُوا أَصْوَاتَكُمْ عِنْدَ مِنْبَرِ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ يَوْمُ الجُمُعَةِ، وَلَكِنْ إِذَا صَلَّيْتُ الجُمُعَةَ دَخَلْتُ فَاسْتَفْتَيْتُهُ فِيمَا اخْتَلَفْتُمْ فِيهِ، فَأَنْزَلَ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ: {أَجَعَلْتُمْ سِقَايَةَ الْحَاجِّ وَعِمَارَةَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ كَمَنْ آمَنَ بِاللهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ} [التوبة: 19] الآيَةَ إِلَى آخِرِهَا.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1879]
المزيــد ...
Daga Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Na kasanace a wurin minbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai wani mutum ya ce:
Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai kawai in shayar da mai yin aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta babu ruwana da in yi wani aiki sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa, sai Umar ya yi musu tsawa, kuma ya ce: Kada ku ɗaga muryarku a wajen mimbarin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali ranar Juma'a ce, sai dai idan na sallaci Juma'a zan shiga in tambaye shi a cikin abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da: {Shin yanzu kwa mayar da shayar da mai aikin Hajj da kuma raya Masallaci mai alfarma kamar wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira}[al-Taubah: 19] karanta ayar har zuwa ƙarshenta.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1879]
Nu'umanu Ibnu Bashir - Allah Ya yarda da su - ya ambaci cewa shi yana zaune a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ji wani mutum yana cewa: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in shayar da mai aikin Hajji. Wani kuma ya ce: Bayan na musulunta ba zan damu dana aikata wani aiki ba sai dai in raya Masallaci mai alfarma. Wani kuma ya ce: Jihadi a tafarkin Allah ya fi abin da kuka faɗa. Sai Umar Ibnul Khaɗɗabi - Allah Ya yarda da shi- ya yi musu tsawa saboda ɗaga muryarsu da suka yi a wajen mimbarin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma safiyar ranar Juma'a ce, sai dai idan na yi sallar Juma'a zan shiga in tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a kan abin da kuka saɓa a cikinsa, sai Allah - Mai girma da ɗaukaka - Ya saukar da:
{Shin, kun mayar da shãyar da mahajjata da rãyar da Masallaci Mai alfarma kamar wanda ya yi ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira, kuma ya yi jihãɗi a cikin hanyar Allah? Bã su daidaita a wurin Allah. Kuma Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai} [al-Tauba: 19].