عَنْ حُذَيْفَةَ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
كُنَّا إِذَا حَضَرْنَا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ طَعَامًا لَمْ نَضَعْ أَيْدِيَنَا حَتَّى يَبْدَأَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَيَضَعَ يَدَهُ، وَإِنَّا حَضَرْنَا مَعَهُ مَرَّةً طَعَامًا، فَجَاءَتْ جَارِيَةٌ كَأَنَّهَا تُدْفَعُ، فَذَهَبَتْ لِتَضَعَ يَدَهَا فِي الطَّعَامِ، فَأَخَذَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ بِيَدِهَا، ثُمَّ جَاءَ أَعْرَابِيٌّ كَأَنَّمَا يُدْفَعُ فَأَخَذَ بِيَدِهِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «إِنَّ الشَّيْطَانَ يَسْتَحِلُّ الطَّعَامَ أَنْ لَا يُذْكَرَ اسْمُ اللهِ عَلَيْهِ، وَإِنَّهُ جَاءَ بِهَذِهِ الْجَارِيَةِ لِيَسْتَحِلَّ بِهَا فَأَخَذْتُ بِيَدِهَا، فَجَاءَ بِهَذَا الْأَعْرَابِيِّ لِيَسْتَحِلَّ بِهِ فَأَخَذْتُ بِيَدِهِ، وَالَّذِي نَفْسِي بِيَدِهِ، إِنَّ يَدَهُ فِي يَدِي مَعَ يَدِهَا».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2017]
المزيــد ...
Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Mun kasance idan muka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ma sanya hannuwanmu har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara sanya hannunsa, kuma mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kunyanga ta zo kai ka ce ana turota ne, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abincin, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo, kai kace ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Shaiɗan yana halatta abin cin da ba'a ambaci sunan Allah a kansa ba, kuma shi (shaidan) ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta shi da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta shi da shi, sai na riƙe hannunsa, lallai hannunsa yana cikin hannuna tare da hannunta».
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2017]
Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa su idan suka halarci abinci tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - basa sanya hannayensu a cikin abin cin har sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara ya sanya hannunsa, cewa mu wani lokaci mun halarci abinci tare da shi, sai wata kuyanga (baiwa) ta zo saboda tsananin saurinta kai ka ce ana turota, sai ta tafi dan ta sanya hannunta a cikin abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya riƙe hannunta, sannan wani balaraben ƙauye ya zo kai ka ce ana turo shi ne, sai ya riƙe hannunsa kafin ya taɓa abin cin, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbat agare shi - ya ce: Lallai Shaiɗan yana samun dama a cikin abin ci idan ya fara cinsa ba tare da ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - ba, lallai ya zo da wannan kuyangar ne dan ya halatta cin abin cin da ita sai na riƙe hannunta, sai ya zo da wannan balaraben ƙauyen dan ya halatta abin cin da shi, sai na riƙe hannunsa, na rantse da wanda raina yake a hannunsa, lallai hannun Shaiɗan yana hannuna tare da hannunta, sannnan ya ambaci sunan Allah ya ci.