عَنْ أَنَسِ بْنِ مَالِكٍ رَضيَ اللهُ عنه قَالَ:
بَيْنَمَا نَحْنُ فِي الْمَسْجِدِ مَعَ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذْ جَاءَ أَعْرَابِيٌّ، فَقَامَ يَبُولُ فِي الْمَسْجِدِ، فَقَالَ أَصْحَابُ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: مَهْ مَهْ، قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَا تُزْرِمُوهُ، دَعُوهُ» فَتَرَكُوهُ حَتَّى بَالَ، ثُمَّ إِنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ دَعَاهُ فَقَالَ لَهُ: «إِنَّ هَذِهِ الْمَسَاجِدَ لَا تَصْلُحُ لِشَيْءٍ مِنْ هَذَا الْبَوْلِ، وَلَا الْقَذَرِ إِنَّمَا هِيَ لِذِكْرِ اللهِ عَزَّ وَجَلَّ، وَالصَّلَاةِ وَقِرَاءَةِ الْقُرْآنِ» أَوْ كَمَا قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: فَأَمَرَ رَجُلًا مِنَ الْقَوْمِ فَجَاءَ بِدَلْوٍ مِنْ مَاءٍ فَشَنَّهُ عَلَيْهِ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 285]
المزيــد ...
Daga Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wata rana muna cikin masallaci tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ga wani balaraben ƙauye ya zo, sai ya miƙe yana fitsari a cikin masallaci, sai sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suka ce: Tsaya tsaya, sai ya ce: Sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
«Kada ku yanke masa fitsarinsa, ku ƙyake shi» sai suka rabu da shi har saida ya gama fitsari, sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kira shi sai ya ce masa: «Lallai waɗannan masallatan badan fitsari aka yi su ba, ko dan ƙazanta , kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka, da sallah da kuma karatun alƙur'ani» ko kamar yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Sai ya umarci wani mutum daga cikin mutanen sai ya zo da guga na ruwa sai ya zuba a kansa.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 285]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin masallacinsa a tare da shi akwai sahabbansa, sai wani balaraben ƙauye ya zo daga ƙauye, sai ya zauna yana yin fitsari a grfen masallaci. Sai sahabbai suka yi masa tsawa suka ce: Tsaya tsaya. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ku ƙyale shi, kada ku yanke masa fitsarinsa, sai suka barshi har sai da ya gama.
Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kirashi sai ya ce masa: Lallai masallatai badan fitsari aka yi su ba, ko nau'ikan ƙazanta ba, kawai su dan ambatan Allah ne - Mai girma da ɗaukaka -, da sallah, da kuma karatun alƙur'ani da makamancin haka. Sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya umarci wani mutum daga cikin sahabbai sai ya zo da guga cike da ruwa sai ya zuba akan fitsarinsa a hankali.