عَنْ أُمِّ عَطِيَّةَ رَضيَ اللهُ عنها قَالَتْ:
تُوُفِّيَتْ إِحْدَى بَنَاتِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَخَرَجَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: «اغْسِلْنَهَا ثَلاَثًا، أَوْ خَمْسًا أَوْ أَكْثَرَ مِنْ ذَلِكَ، إِنْ رَأَيْتُنَّ بِمَاءٍ وَسِدْرٍ، وَاجْعَلْنَ فِي الآخِرَةِ كَافُورًا -أَوْ شَيْئًا مِنْ كَافُورٍ-، فَإِذَا فَرَغْتُنَّ فَآذِنَّنِي»، قَالَتْ: فَلَمَّا فَرَغْنَا آذَنَّاهُ، فَأَلْقَى إِلَيْنَا حِقْوَهُ، فَقَالَ: «أَشْعِرْنَهَا إِيَّاهُ»، وَقَالَتْ: وَجَعَلْنَا رَأْسَهَا ثَلاَثَةَ قُرُونٍ.
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 1258]
المزيــد ...
Daga Ummu Aɗiyya - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Ɗaya daga cikin ’ya’yan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi mata - ta rasu, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita sai ya ce: «Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko sama da haka idan kuna ganin hakan, da ruwa da magarya, ku sanya kafur a na ƙarshe - ko wani abu daga kafur -, idan kun gama ku sanar da ni», ta ce: Yayin da muka gama sai muka sanar da shi, sai ya jeho mana mayafinsa, sai ya ce: «Ku sanya shi ɗanfare da jikinta», kuma ta ce: Kuma muka sanya kanta naɗi uku.
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 1258]
Zainab 'yar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta rasu, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga wurin matan da zasu yi mata wanka, sai ya ce da su: Ku wanketa da ruwa da magarya mara sau uku, ko sau biyar ko sama da haka, idan akwai buƙatuwar hakan, ku sanya wani abu daga kafur a na ƙarshen, idan kun gama to ku sanar da ni. Yayin da suka gama wanketa sai suka sanar masa, sai ya baiwa masu wankewar mayafinsa, kuma ya ce: Ku yi mata likkafani a cikinsa kuma ku sanya shi shi ne tufan da zai bi jikinta, sannan aka tufka gashin kanta tufka uku.