kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

1. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance damantawa tana kayatar da shi, a sanya takalminsa, da taje kansa, da tsarkinsa, kai da sha'aninsa duka
عربي Turanci urdu
2. Daga ciki akwai fadin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare cikin hadisin ceto:
عربي Turanci urdu
3. Ban taɓa ganin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ƙyaƙyata dariya ba, har inga ƙarshen ganɗarsa ba, kawai ya kasance yana murmushi
عربي Turanci urdu
4. Kada ku yi salla a kanku. Kada kuyi addu’a akan yayan ku, kar ku kira kudin ku, kar ku yarda da Allah na awa daya da aka gabatarda kudiri kuma zai amsa muku
عربي Turanci urdu
5. Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba
عربي Turanci urdu
6. Wanda ya reni 'yan mata biyu har suka balaga zai zo ranar alƙiyama ni da shi" sai ya dunƙule yatsunsa
عربي Turanci urdu
7. Da ba dan kar na tsanantawa muminai ba - ko ga: al'ummata ba - dana umarce su da yin asuwaki a yayin kowace sallah
عربي Turanci urdu
8. Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)
عربي Turanci urdu
9. Na kasance tare da Sa'eed bin Jubair sai ya ce: Wanene a cikinku ya ga duniyar da ta share jiya? Na ce: Ni ne, sai na ce: Amma ni ba na cikin sallah, amma an yi min duri
عربي Turanci urdu
10. Ku kusanto ku daidaita, ku sani cewa babu wani daga cikinku da zai tsira da aikinsa". Suka ce: Ya Manzon Allah koda kaine?ya ce: "Koda nine sai dai idan Allah Ya lulluɓeni da rahamarSa da kuma falalarSa
عربي Turanci urdu
11. Ya Allah ina neman tsari da yardarKa daga fushinKa, da kuma rangwaminKa daga uƙubarKa, kuma ina neman tsari da Kai daga gareKa ba zan iya ƙididdige yabo gareKa ba kamar yadda Ka yabi kanKa
عربي Turanci urdu
12. Shin ba zan baku labarin 'yan aljanna ba? Duk mai rauni da ake rainawa, da zai rantse da Allah zai kuɓutar da shi, shin ba zan baku labarin 'yan wuta ba? duk mai ƙaton ciki mai kaushin rai mai girman kai
عربي Turanci urdu
13. 'Lallai Ni na san wata kalmar da zai faɗeta da abinda yake ji ya tafi daga gare shi, da zaice: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan, abinda yake ji zai tafi
عربي Turanci urdu
14. Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba
عربي Turanci urdu
15. Na ce: Ya Manzon Allah menene tsira? ya ce: "Ka mallaki harshenka gareka, kuma gidanka ya yalwaceka, ka yi kuka akan kuskurenka
عربي Turanci urdu
16. Akwai matakai guda dari a Sama wanda Allah ya tanadar wa mujahidai a tafarkin Allah, tsakanin darajoji biyu kamar tsakanin sama da kasa
عربي Turanci urdu
17. Ni ina inda zatan bawaNa yake, kuma Ni ina tare da shi lokacin da yake ambatona - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
18. Na tambayi Nana A'isha, na ce: Da wane abu Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yakasance yake farawa idan ya shiga gidansa? ta ce: Da asuwaki
عربي Turanci urdu
19. An anbaci wani mutum da ya yi bacci a darensa har saida ya wayi gari a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: "Wancan wani mutum ne wanda Shaiɗan ya yi fitsari a cikin kunnuwansa, ko ce ya yi: A cikin kunnensa
عربي Turanci urdu
20. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ƙoƙari a cikin goman ƙarshe irin ƙoƙarin da ba ya yi a cikin waninsa
عربي Turanci urdu
21. Mun kasance muna shirya wa Manzon Allah - Salati da amincin Allah su tabbata a gare shi - kayan aikin sa da tsarkake shi, saboda haka Allah zai aiko masa da duk abin da yake son ya aiko daga dare, don haka sai ya sa su daidai, ya yi alwala ya yi sallah.
عربي Turanci urdu
22. Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama
عربي Turanci urdu
23. Lallai kada ɗayanku ya mutu sai yana kyautatawa Allah zato
عربي Turanci urdu
24. Idan ka kasance kamar yadda ka faɗa, to, kamar kana cusa musu toka mai zafi ne a bakin su, kuma wani mai rinjaye a kansu daga Allah ba zai gushe tare da kai ba muddin dai ka kasance a kan haka
عربي Turanci urdu
25. Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi
عربي Turanci urdu
26. Babu wasu mutane da suke tashi daga wani wurin zaman da ba sa ambaton Allah a cikinsa, face sun tashi kamar mushen jaki, kuma suna masu asara
عربي Turanci urdu
27. Misalin wanda yake ambatan Ubangijinsa da wanda ba ya ambatan Ubangijinsa, kamar rayayye ne da matacce
عربي Turanci urdu
28. Lallai ni ina jiye muku tsoro a baya na, abinda za'a buɗe muku na ƙawar duniya da adonta - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
29. Wanda yake son Allah Ya tseratar da shi daga baƙin cikin ranar Alƙiyama, to, ya yaye wa wanda yake cikin wani mawuyacin hali, ko ya sarayar masa (wani haƙƙi ko nauyin da ya ke kansa)
عربي Turanci urdu
30. Lallai cewa mafi sauƙin 'yan wuta a azaba wanda yake da takalma biyu da igiyoyi na wuta, ƙwaƙwalwarsa tana tafarfasa kamar yadda (tukunyar) tagulla take tafarfasa, ba ya ganin cewa wani mutum ya fi shi tsananin azaba, kuma shi shi ne mafi sauƙin azabarsu
عربي Turanci urdu
31. Za'a kusanto da mumini ranar alƙiyama daga Ubangijinsa - Mai girma da ɗaukaka - har sai ya sanya kiyayewarSa, sai Ya tabbatar masa da zunubansa
عربي Turanci urdu
32. Ka Guji Duniya Sai Allah ya so ka, ka guji abin hannun Mutane sai Mutane su so ka
عربي Turanci urdu
33. Aikin alheri (shi ne) kyakkyawar ɗabi'a, zunubi kuma abinda ya sosu a cikin ƙirji, kuma kaƙi mutane su yi tsinkaye akansa
عربي Turanci urdu
34. Za a shigar da Jahannama a wannan rana a kansa saboda iyayengiji dubu saba'in, tare da kowace sarauta ta sarakuna dubu saba'in da suke jan ta - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
35. Baka ga Wasu Ayoyi da aka saukar da su ba a wannan Daren ba'a tava ganinsu ba? Falaqi da Nasi
عربي Turanci urdu
36. Allah baya karvar Sallar Wacce ta isa Haila sai da Hijabi - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
37. Kuna yin hamma yayin sallah daga Shaidan, don haka idan wani daga cikinku yayi hamma, to, ya bar shi gwargwadon iyawarsa
عربي Turanci urdu
38. An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
39. Wanda ya yi azumin wani yini a tafarkin Allah, Allah Zai nisantar da fuskarsa daga wuta (tsawon) shekara saba'in
عربي Turanci urdu
40. Mutane ba zasu gushe ba cikin alheri matuƙar sun gaggauta buɗa baki
عربي Turanci urdu
41. Mun kasance muna fitar da zakkar fidda kai lokacin da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cikinmu, daga kowane ƙaramin (yaro) da babba, ɗa ne ko bawa, Sa’i na abinci, ko Sa’i na cukwi, ko Sa’i na sha'ir, ko Sa’i na dabino, ko Sa’i na zabibi
عربي Turanci urdu
42. Mun yi sahur tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan ya tashi zuwa sallah, na ce: Nawa ne tsakanin kiran sallah da sahur? ya ce: Gwargwadan ayoyi hamsin
عربي Turanci urdu
43. Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana i'itikafin goman ƙarshe na Ramadan, har Ya koma ga Allah , sannan matansa suka yi i'itikafi a bayansa
عربي Turanci urdu
44. Ku yi sahur, domin lallai cewa akawai albarka a cikin sahur - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
45. Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi
عربي Turanci urdu
46. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya wajabta zakkar fidda kai, Sa'i na dabino, ko Sa'i na alkama, akan bawa da ɗa, namiji da mace, ƙarami da babba cikin musulmai, kuma ya yi umarni a bada ita kafin fitar mutane zuwa sallah
عربي Turanci urdu
47. Ba ya halatta ga wata mace musulma ta yi tafiyar dare (ɗaya) sai a tare da ita akwai namiji muharraminta
عربي Turanci urdu
48. Wanda ya manta alhali yana azumi, sai ya ci ko ya sha, to ya cike aziminsa, kaɗai Allah ne Ya ciyar da shi kuma Ya shayar da shi
عربي Turanci urdu
49. Mun halarci idi tare da Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - sai ya ce: "Waɗannan kwanaki biyun Mazon Allah - tsira da Amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana azimtarsu: Ranar buɗa bakinku daga aziminku, ɗaya ranar kuma kuna cin abin layyarku a cikinta
عربي Turanci urdu
50. Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya
عربي Turanci urdu
51. Ku yi kirdadon daren Lailatul-ƙadri a cikin mara daga goman ƙarshe na Ramadan
عربي Turanci urdu
52. Ina ganin mafarkenku haƙiƙa sun haɗu a bakwan ƙarshe, duk wanda ya kasance zai yi kardadonsa to ya yi kardadonsa a bakwan ƙarshe
عربي Turanci urdu
53. Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne
عربي Turanci urdu
54. Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama
عربي Turanci urdu
55. Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
56. Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kuɓuta daga mai ɗaga murya da mai aske kanta da mai tsaga kayanta
عربي Turanci urdu
57. Banu Isra'il sun kasance Annabawa ne suke shugabantarsu, duk lokacin da wani Annabi ya rasu sai wani Annabin ya maye gurbinsa, lallai cewa babu wani Annabi a baya na, za'a samu halifofi zasu yawaita
عربي Turanci urdu
58. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan goman ƙarshe ta shiga zai raya dare, zai farkar da iyalansa, zai yi ƙoƙari zai ɗaure gwabso
عربي Turanci urdu
59. Ibada a cikin rashin zaman lafiya kamar hijira ce zuwa gareni
عربي Turanci urdu
60. Babu wani musulmi da zai yi wata addu'a wacce babu zunubi a cikinta, kuma babu yanke zumunci, face sai Allah Ya ba shi ɗayan abu uku: Kodai Ya gaggauto masa da (amsa) addu’ar sa, ko kuma Ya tanadar masa ita sai ranar alƙiyama, ko kuma Ya kawar masa da wani mummunan abu irinta". Sai (Sahabbai) suka ce: Kenan mu yawaita? Sai ya ce: "Allah Shi ne Mafi yawaitawa
عربي Turanci urdu
61. Cewa Annabin Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cewa a lokacin baƙin ciki: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mai girma kuma Mai haƙuri, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Ubangijin al'arshi mai girma, babu wani abin bauta da gaskiya sai Allah, Ubangijin sammai, Ubangijin ƙasa, kuma Ubangijin al'arshi mai girma
عربي Turanci urdu
62. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓayin wata sallah ba bayan saukar: {Idan nasarar Allah ta zo da buɗi} [al-Nasr: 1] ta sauka gare shi sai ya ce a cikinta (sallar): "Tsarki ya tabbatar maKa Ubangijinmu da godiyarKa ya Allah Ka gafarta mini'
عربي Turanci urdu
63. Idan ɗayanku zai yi hamma to ya riƙe bakainsa da hannunsa, domin cewa Shaiɗan yana shiga
عربي Turanci urdu
64. Haƙƙin musulmi akan musulmi guda shida ne" aka ce: Waɗannene su ya Manzon Allah?, ya ce: "Idan ka haɗu da shi to ka yi masa sallama, idan ya kiraka ka amsa masa, idan ya nemi nasiharka to ka yi masa nasiha, idan ya yi atishawa sai ya godewa Allah to ka gaishe shi, idan ya yi rashin lafiya to ka duba shi, idan ya mutu to kabi shi (ka bi jana'izarsa) - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
65. Allah ba Ya duba zuwa wanda ya ja tufansa (ƙasa) dan girman kai
عربي Turanci urdu
66. Wanda ya yanki haƙƙin wani mutum musulmi da rantsuwarsa, to haƙiƙa Allah Ya wajabta wuta gare shi, kuma Ya haramta masa aljanna" sai wani mutum ya ce: Koda wani abune ɗan kaɗan ya Manzon Allah? ya ce: "Koda kara ne na itaciyar ƙirya
عربي Turanci urdu
67. Ni'imomi biyu ana yi wa da yawa daga mutane kamunga a cikinsu: Lafiya da rarar lokaci
عربي Turanci urdu
68. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa
عربي Turanci urdu
69. Lallai masu yawaita tsinuwa ba sa zama masu shaida ko masu ceto a ranar alƙiyama
عربي Turanci urdu
70. Lalle Ubangijinku Mai kunya ne kuma Mai karamci ne, Yana jin kunyar bawanSa idan ya ɗaga hannayensa zuwa gare Shi Ya dawo da su babu komai
عربي Turanci urdu
71. Wasu mutane basu zauna a wani wurin zama ba basu ambaci Allah a cikinsa ba kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba sai hasara ta kasance a kansu, idan (Allah) Ya so Ya azabtar da su idan kuma Ya so Ya gafarta musu
عربي Turanci urdu
72. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana son Addu'ar da ta tattaro komai, kuma yana ƙyale wacce ba ita ba
عربي Turanci urdu
73. Rantsuwa mai sa anfani ce a haja (kayan sayarwa), kuma mai shafe albarkar riba ce
عربي Turanci urdu
74. Kada ku zagi Iska, idan kuka ga abinda ba kwa so to kuce: Ya Allah mu muna roƙonKa daga alherin wannan iskar, da alherin abinda ke cikinta, da alherin abinda aka umarce ta da shi, kuma muna neman tsarinKa daga sharrin wannan iskar, da kuma sharrin abinda ke cikinta, da kuma sharrin abinda aka umarce ta da shi
عربي Turanci urdu
75. Kada ɗayanku ya ce: Ya Allah Ka gafarta mini in Ka so, Ka yi mini rahama in Ka so, Ka azirtani in Ka so, ya ƙudirce niyyar rokonsa, lallai Shi Yana aikata abinda Yake so, babu mai tilasta Shi
عربي Turanci urdu
76. An turbuɗe hancin mutumin da aka ambaceni a wurinsa bai yi mini salati ba, an turbuɗe hancin mutumin da Ramadan ya shiga sannan ya fita ba’a gafarta masa ba, kuma an turbuɗe hancin mutumin da mahaifansa suka tsufa a wurinsa amma basu shigar da shi aljanna ba
عربي Turanci urdu
77. Wanda ya azimci zamani (a here) to bai yi azimi ba, azimin kwana uku azimin zamani ne gaba ɗayansa
عربي Turanci urdu
78. Me ya samu wasu mutane ne sun ce kaza da kaza? sai dai cewa ni ina sallah kuma ina bacci, ina azimi ina buɗe baki, kuma ina auren mata, wanda ya ƙi sunnata to ba ya tare da ni
عربي Turanci urdu
79. Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
80. Wanda ya haddace ayoyi goma daga farkon Suratul Kahf, za'a tsare shi daga Dujal". A cikin wata riwayar: "Daga ƙarshen Suratul Kahf
عربي Turanci urdu
81. Wanda ya duba mara lafiya (wanda) ajalinsa bai yi ba, sai ya ce a wurinsa sau bakwai: Ina roƙon Allah Mai girma Ubangijin al-Arshi Mai girma Ya baka lafiya, sai Allah Ya ba shi lafiya daga wannan cutar
عربي Turanci urdu
82. Lallai cewa zukatan 'ya'yan Adam dukkansu (suna) tsakanin yatsu biyu daga yatsun (Ubangiji) al-Rahman, kamar zuciya ɗaya, yana jujjuyata yadda Ya so
عربي Turanci urdu
83. Ba'a taɓa ba wa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - zabi ba tsakanin abubuwa biyu face sai ya zaɓi mafi sauƙinsu, matuƙar bai kasance saɓo ba, idan ya kasance saɓo ne to ya kasance ya fi kowa nisantar shi
عربي Turanci urdu
84. Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji
عربي Turanci urdu
85. Allah Zai tara mutane na farko da na ƙarshe a bigire ɗaya, mai kira zai jiyar da su kuma gani zai ƙetare su, rana zata kusanto, sai baƙin ciki da takaici ya kai ga mutane abinda ba za su iya ɗauka ba, kuma ba za su iya jurewa ba
عربي Turanci urdu
86. Lallai mumini yana da wata shema a cikin aljanna ta lu'ulu'u ɗaya mai ƙofa a cikinta, tsawonta mil sittin ne, mumini yana da mata a cikinta, mumini zai kewayesu amma sashinsu ba zai ga sashi ba
عربي Turanci urdu
87. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tsinewa namijin da ya sanya kayan mace, da macen da ta sanya kayan namiji
عربي Turanci urdu
88. Wanda ya kasance yana da abin yankan da zai yanks shi (na Layya) to idan jijirin watan Zul-Hijja ya kama, to kada ya cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai ya yi layya
عربي Turanci urdu
89. Idan (watan) Ramadan ya zo sai a buɗe ƙofofin aljanna, kuma a kukkule ƙofofin wuta, a ɗaɗɗaure shaiɗanu
عربي Turanci urdu