«لن يدخلَ النارَ رجلٌ شَهِد بدرًا والحُدَيْبِيَة».
[صحيح] - [رواه أحمد، وأصله في صحيح مسلم] - [مسند أحمد: 15262]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Duk mutumin da ya halarci (yaƙin) Badar da Hudaibiyya ba zai shiga wuta ba".
-
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa duk wanda ya halarci yaƙin Badar wanda aka yi a cikin shekara ta biyu da hijira yana mai yaƙi tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haka nan wanda ya halarci Sulhun Hudaibiyya, kuma a cikinsa ne aka yi Bai'atir Ridwan wacce aka yi a cikin shekara ta shida da hijira ba zai shiga wuta ba.