1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba

عَنْ أَبِي قَتَادَةَ رضي الله عنه قَالَ: قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ:

«الرُّؤْيَا الصَّالِحَةُ مِنَ اللَّهِ، وَالحُلُمُ مِنَ الشَّيْطَانِ، فَإِذَا حَلَمَ أَحَدُكُمْ حُلُمًا يَخَافُهُ فَلْيَبْصُقْ عَنْ يَسَارِهِ، وَلْيَتَعَوَّذْ بِاللَّهِ مِنْ شَرِّهَا، فَإِنَّهَا لاَ تَضُرُّهُ».

Daga Abu Katadah- Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Mafarki na gari daga Allah ne, mummunan mafarki kuwa daga Shaiɗan ne, idan ɗayanku ya yi mummunan mafarkin da yake jin tsoronsa to ya yi tofi a hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, to cewa shi ba zai cutar da shi ba".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 3292

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, mummunan mafarki shi ne mafarkin da yake ƙi kuma yake baƙanta rai to daga Shaiɗan ne.
Wanda ya ga abinda yake ƙinsa (a mafarki) to ya yi tofi a ɓangaren hagunsa, kuma ya nemi tsarin Allah daga sharrinsu; to cewa shi ba zai cutar da shi ba, inda Allah Ya sanya abinda aka ambata (na Addu’a) sababi ne na kuɓuta daga abin ƙi na abinda jeranta akan mafarki.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Kyakkyawan mafarki da mummuna wani abu ne daga abinda mai barci yake ganinsa a cikin barcinsa na abubuwa, sai dai (Kalmar: Ru'uya) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na alheri da abu mai kyau, kuma (Kalmar: Hulum) ta fi rinjaye akan abinda yake ganinsa na sharri da mummuna, kuma ana anfani da kowane ɗayan daga cikinsu a bigiren ɗayan.
  2. Rabe-raben mafarki: 1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa. 2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke. 3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam.
  3. Abinda aka ambata a taƙaice daga Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku: Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
  4. Abinda aka ambata a taƙaice daga laduban mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar: Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa shi, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to cewa shi ba zai cutar da shi ba.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
kashe kashe