1. Gida
  2. kashe kashe

Sabuntawa An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali

عن علي رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:

«رُفِعَ الْقَلَمُ عن ثلاثة: عن النائم حتى يَسْتَيْقِظَ، وعن الصبي حتى يَحْتَلِمَ، وعن المجنون حتى يَعْقِلَ».

Daga Aliyu - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"An ɗauke alƙalami ga mutum uku: Mai Bacci har sai ya farka, da yaro har sai ya balaga, da kuma mahaukaci har sai ya yi hankali".

الملاحظة
رفع القلم لي ثلاث عن صبي حتى يبلغ وعن ناءم حتى يستيقظ وعن مجنون حتى يبرأ السلام عليكم
النص المقترح عن علي رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:«رُفِعَ الْقَلَمُ عن ثلاثة: عن النائم حتى يَسْتَيْقِظَ، وعن الصبي حتى يَحْتَلِمَ، وعن المجنون حتى يَعْقِلَ».

Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i cikin alkubra da Ibnu Majah haka kuma Ahmad Sunan Abi Dawud - 4403

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin Dora hukunci na (shari'a) wanda yake lazimtar 'ya'yan Adam ne sai waɗannan ukun:
Ƙaramin yaro har sai ya girma ya balaga.
Da mahaukaci wato mara hankali har sai hankalinsa ya dawo gare shi .
Da mai bacci har sai ya farka.
Ɗora shari'a haƙiƙa an ɗauke musu ita, kuma aikata laifinsu ba'a rubuta musu, sai dai ana rubuta alheri ga yaro ƙarami banda mahaukaci da mai bacci; domin su suna cikin wadanda ibadarsu ba ta inganta ba daga gare shi saboda gushewar ji.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rashin cancantar mutum yana zama kodai saboda baccin da rashin farkawa ya sarayar masa da wajibansa, ko saboda ƙarancin shekaru da yarinta wanda hakan ya sa ya rasa cancanta, ko saboda haukan da ayyukansa na hankali suka raurawa tare da shi, ko abinda yake riskarsa kamar maye, wanda ya rasa banbancewa da fayyacewa ingantacciya, to cancanta ta koru daga gare shi saboda sababi daga waɗannan sabubban uku; domin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - saboda adalcinSa, da haƙurinSa, da kyautarSa, haƙiƙa Ya ɗauke masa kamun abinda yake bijirowa daga gare shi na wuce gona da iri ko gajiyawa a cikin hakkin Allah - Maɗaukakin sarki -.
  2. Rashin rubuta zunubai akansu, ba ya kore tabbatar da hukunce-hukunce na duniya akansu; kamar mahaukaci da zai yi kisa, to babu sakayya akansa kuma babu kaffara, amma akwai diyya akan 'yan uwansa.
  3. Balaga tana da almomi biyar: Fitar maniyyi, ta hanyar mafarki da waninsa, ko tsirowar gashin mara, ko cika shekara goma sha biyar, mace ta ƙara al'amari na huɗu: Shi ne haila.
  4. Al-Subki ya ce: Ƙaramin yaro shi ne yaro. Waninsa ya ce; Yaro a cikin mahaifyarsa ana ambatansa ɗan tayi, idan aka haife shi to ya zama yaro, idan an yaye shi to ya zama yaro har zuwa shekara bakwai, sannan ya zama mai tasowa har zuwa shekara goma sannan ƙaƙƙarfan yaro, wanda ake yankewa da shi cewa ana ambatansa yaro a cikin waɗannan halayen gaba ɗayansu, Suyuɗine ya faɗe shi.

Manufofin Fassarorin

52 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ID Indonesia الإندونيسية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
kashe kashe