kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

1. Cewa an samu wata mace a wasu daga yakokin Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi a kashe, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana kashe mata da yara
عربي Turanci urdu
2. ya yi hani daga bakance, ya ce: "Lallai shi ba ya zuwa da alheri, kawai ana fitar da shi ne daga marowaci
عربي Turanci urdu
3. Lallai ni wallahi - in Allah Ya so - bana rantsuwa, sai inga waninta mafi alheri daga gareta. sai na yi kaffarar rantsuwata, kuma nazowa wanda shi ne mafi alherin - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
4. Wanda ya sanya alhariri a duniya ba zai sanya shi a lahira ba
عربي Turanci urdu
5. Yana daga mafi girman jihadi kalmar adalci a a gaban azzalumin sarki
عربي Turanci urdu
6. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki
عربي Turanci urdu
7. Mai tsira da amincin Allah ya hana yin salla bayan Asuba har sai rana ta hudo, haka nan bayan 'La'asar har sai ta fadi
عربي Turanci urdu
8. Cewa wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - daga alkiyama, sai ya ce: Yaushe ne alkiyama? Ya ce: "Mai ka tanadar mata?
عربي Turanci urdu
9. Mutum yana kan Addinin abokinsa, saboda haka dayanku ya duba wanda zai yi abokantaka (da shi)
عربي Turanci urdu
10. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yawaita faɗin: "Ya mai jujjuya zukata Ka tabbatar da zuciyata akan addininKa
عربي Turanci urdu
11. Idan kare ya sha a kwaryar ɗayanku to ya wanketa sau bakwai
عربي Turanci urdu
12. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, azaba ta tabbata ga larabawa daga sharrin da ya kusanto, a yau an buɗe katangar Yajuju da Majuju kwatankwacin hakan
عربي Turanci urdu
13. Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi tsananin kunya daga budurwar dake cikin budircinta, idan ya ga wani abinda yake kinsa muna gane hakan a fuskarsa
عربي Turanci urdu
14. Wanda ya roki Allah shahada da gaskiya, Allah Zai kai shi matsayin shahidai, koda ya mutu akan shinfiɗarsa
عربي Turanci urdu
15. Bala'i ba zai gushe ga mumini da mumina ba a kansa da ɗansa da dukiyarsa har sai ya gamu da Allah ba shi da wani laifi
عربي Turanci urdu
16. Mafi kusancin lokacin da bawa yake kasancewa kusa da Ubangiji a cikin (kason) dare na karshe
عربي Turanci urdu
17. Za’a zo da mutum ranar Alkiyama, sai a jefa shi a cikin wuta, sai hanjin cikinsa su fita, sai ya kewaya da su kamar yadda jaki yake kewaye da dutsen nika
عربي Turanci urdu
18. Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta
عربي Turanci urdu
19. Duk wanda ya shirya mayaki a tafarkin Allah to hakika ya yi yaki, wanda ya maye gurbin wani mayaki a tafarkin Allah (a gidansa) da alheri to hakika ya yi yaki
عربي Turanci urdu
20. Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi
عربي Turanci urdu
21. An bani abubuwa biyar, wadanda ba a baiwa wani daga cikin (Annabawa) a gabani na ba
عربي Turanci urdu
22. bayan kowace sallah kada ka bar faɗin: Ya Allah Ka taimakeni akan ambatanKa da gode maKa da kyakkyawar ibadarKa
عربي Turanci urdu
23. Allah Ya ce: Dukkan aikin ɗan Adam nasa ne, sai azimi, lallai shi nawa ne kuma nine zan yi sakayya da shi - 10 ملاحظة
عربي Turanci urdu
24. Idan ɗayanku ya haɗu da ɗan uwansa to ya yi masa sallama, idan bishiya ko katanga ko dutse ya tsare tsakaninsu sannan ya haɗu da shi to ya yi masa sallama kuma
عربي Turanci urdu
25. Shaiɗan yana ƙulli uku akan ƙarshen kan ɗayanku idan ya yi bacci, yana buga (hannunsa) akan kowane ƙulli, ka yi dare mai tsawo, sai ka yi bacci
عربي Turanci urdu
26. Idanun da wuta bata taba su ba: ido mai kuka saboda tsoron Allah, ido mai kiyaye hanyar Allah.
عربي Turanci urdu
27. Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce
عربي Turanci urdu
28. Haƙiƙa ka tambayeni daga wani abu mai girma, kuma shi mai sauƙi ne ga wanda Allah Ya sawwaƙa masa
عربي Turanci urdu
29. Yaku mutane ! Lallai Allah Mai tsarki ne ba Ya karba sai mai tsarki, kuma Allah Ya umarci muminai da abinda Ya umarci Manzanni da shi - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
30. Badaɗayina - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mini wasicci da (abubuwa) uku: Azimin kwana uku a kowane wata, da raka'o'i biyu na walaha, kuma in yi witiri kafin na yi bacci
عربي Turanci urdu
31. Idan kun ga shi to ku yi azimi, idan kun gan shi ku busha ruwa, idan an ɓoye muku (shi) to ku kaddara (kwanakinsa) sa
عربي Turanci urdu
32. Yana daga abin da mutane suka riska daga zancen Annabci na farko: Idan ba ka da kunya, to ka aikata abin da kake so
عربي Turanci urdu
33. Ka bar abinda kake kokwantansa zuwa abinda baka kokwantansa, domin gaskiya nutsuwa ce, kuma ƙarya kokwanto ce
عربي Turanci urdu
34. Ka kasance a duniya kamar kai baƙo ne ko mai ƙetare hanya
عربي Turanci urdu
35. Kada harshenka ya gushe yana ɗanye daga ambatan Allah
عربي Turanci urdu
36. Kada ka kashe shi, domin cewa in ka kashe shi to shi yana matsayinka kafin ka kashe shi, kuma kai kana matsyinsa kafin ya fadi kalmarsa wacce ya fadeta
عربي Turanci urdu
37. Wanda ya ci tafarnuwa ko albasa, to ya yi nesa damu - ko cewa ya yi: Ya yi nesa da - masallacinmu, ya zauna a gidansa
عربي Turanci urdu
38. Zan bada wannan tutar ga wani mutum mai ƙaunar Allah da ManzonSa, Allah zai yi buɗi ta hannayensa
عربي Turanci urdu
39. Ku ji, kuma ku bi, kaɗai abinda aka ɗora musu yana kansu, kuma abinda aka ɗora muku yana kanku
عربي Turanci urdu
40. Zagin musulmi fasiƙanci ne, kuma yaƙarsa kafirci ne
عربي Turanci urdu
41. Kada ku farawa Yahudawa ko Nasara da sallama, idan kun haɗu da ɗayansu a hanya to ku buƙace shi zuwa mafi ƙuncinta
عربي Turanci urdu
42. Wanda ya mari kunci, kuma ya yaga aljihuna, kuma ya yi ihu irin ta Jahiliyya to ba shi tare da mu
عربي Turanci urdu
43. Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka
عربي Turanci urdu
44. Marowaci shi ne wanda aka ambace ni a wurinsa bai yi mini salati ba - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
45. Wanda ya yi sammako zuwa masallaci ko ya maraita, Allah zai tanadar masa wani masauki a cikin aljanna duk lokacin da ya yi sammako ko ya maraita
عربي Turanci urdu
46. Ba'a dawo da addu'a tsakanin kiran sallah da iƙama - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
47. ’’ Ya Allah Ka gyara mini Addini na wanda shi ne ƙashin bayan al’amari na - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
48. Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena da wautata, da wuce gona da irina a cikin dukkan al'amarina, da abinda Kaine Mafi sani da shi daga gareni, ya Allah Ka gafarta mini kurakuraina, da gangancina da jahilcina da kakacina, dukkan hakan daga garenin ne, ya Allah Ka gafarta mini abinda na gabatar da abinda na jinkirtar, da abinda na ɓoye da abinda na bayyana, kaine Mai gabatarwa kuma Kaine Mai jinkirtarwa, kuma kaine Mai iko akan dukkan komai
عربي Turanci urdu
49. Ya Allah lallai ni ina roƙonKa lafiya a duniya da lahira - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
50. Ya Allah ina roƙon Ka dukkan alheri, magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba, kuma ina neman tsarinKa daga dukkan sharri magaggaucinsa da majinkircinsa, abin da na sani daga gare shi da abin da ban sani ba
عربي Turanci urdu
51. Ya Allah ina neman tsarinKa daga gushewar ni'imarKa, da juyawar lafiyarKa, da shammatar azabarKa, da dukkan fushinKa
عربي Turanci urdu
52. Ya Allah ni ina neman tsarinKa daga rinjayar bashi, da rinjayar maƙiyi, da dariyar maƙiya
عربي Turanci urdu
53. Ya Allah da (kiyayyewar) Ka ne muka wayi gari, kuma da (kiyayewar) Ka ne muka shiga maraice, da (al'amarin) Ka ne muka rayu, kuma da (al'amarin) Ka ne zamu mutu, kuma tashi (daga ƙabari) yana gareKa
عربي Turanci urdu
54. Na haneku da shiga wurin mata" sai wani mutum daga mutanen Madina ya ce: Ya Manzon Allah, shin kana ganin ƙanin miji fa? ya ce: "Ƙanin miji (shi ne) mutuwa - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
55. Azirfa da zinare riba ne, sai hannu da hannu, alkama da alkama riba ne, sai hannu da hannu, sha'ir da sha'ir riba ne, sai hannu da hannu, dabino da dabino riba ne, sai hannu da hannu
عربي Turanci urdu
56. ka ce Ya Allah Ka shiryar dani Ka datar dani, ka ambaci shiriya (irin) shiriyarka ta hanya, da dacewa (irin) dacewar kibiya
عربي Turanci urdu
57. Ka sanya hannunka akan wurin da kake jin raɗaɗin daga jikinka, ka ce: Da sunan Allah sau uku, kuma ka ce sau bakwai “Ina nema tsarin Allah da ikonSa daga sharrin abinda nake ji kuma nake tsoro
عربي Turanci urdu
58. Wanda ya ce: Da suna Allah wanda wani abu ba ya cutuwa tare da sunanSa a cikin ƙasa, ko cikin sama, Shi ne Mai yawan ji Masani”. sau uku, wani bala'i na fuj'a ba zai same shi ba har sai ya wayi gari
عربي Turanci urdu
59. Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba
عربي Turanci urdu
60. Babu wani mutum da zai yi mini sallama har sai Allah Ya dawo mini da raina har sai na mayar masa da sallamar
عربي Turanci urdu
61. Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci
عربي Turanci urdu
62. Babu wani ma'abocin zinare ko azirfa, da ba ya bada haƙƙinsu daga garesu, sai a ranar alƙiyama ya kasance za'a ƙerasu a siffar alluna na wuta - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
63. Lallai Bawa idan ya La'anci wani abu, sai la'antar ta tashi zuwa sama, sai a rufe kofofin Sama a hanata shiga, sannan sai ta dawo Qasa, sai a toshe mata kofa, sai ta duda hagu da Dama, idan bata samu wurin da ta dace ta sauka ba sai ta koma kan wandaaka yiwa ita, to idan ya dace da ita shi ke nan idan kuma bai dace ba sai ta koma kan wanda yayi ta
عربي Turanci urdu
64. Mai kira zai kira: Lallai cewa ku zaki yi lafiya ba za ku yi masassara ba har abada, kuma ku zaku rayu ba za ku mutu ba har abada, kuma cewa ku zaku samartaku ba zaku tsufaba har abada, kuma cewa ku zaku ni'imtu ba zaku yanke ƙauna ba har abada'
عربي Turanci urdu
65. Idan 'yan aljanna suka shiga aljanna, ya ce: Allah -Maɗaukakin sarki - zai ce: Kuna son wani abu ne da zan ƙaro muku shi?
عربي Turanci urdu
66. Shi ruwansa mai tsarkakewa ne, kuma mushensa halal ne
عربي Turanci urdu
67. Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa
عربي Turanci urdu
68. Idan ɗayanku ya farka daga baccinsa to ya face hancinsa sau uku, domin cewa Shaiɗan yana kwana akan karan hancinsa
عربي Turanci urdu
69. Idan dayanku ya yi alwala kuma ya sanya huffinsa to ya yi sallah da su, kuma ya yi shafa akansu, sannan kada ya ciresu in ya so sai dai saboda janaba
عربي Turanci urdu
70. Wani mutum ba zai jefi wani mutum da fasiƙanci ba, kuma ba zai jefe shi da kafirci ba, sai ta dawo kansa idan m'abocinta bai zama kamar hakan ba
عربي Turanci urdu
71. Lallai Shaiɗan haƙiƙa ya yanke ƙaunar masu sallah su bauta masa a tsibirin larabawa, sai dai a sa gaba a tsakaninsu
عربي Turanci urdu
72. Cewa Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata agareshi ya kasance baya Mummunan zato - 3 ملاحظة
عربي Turanci urdu
73. Wanda ya rantse da amana to baya daga cikinmu
عربي Turanci urdu
74. Yaku wannan mata, ku yi sadaka, dan ni an nuna min cewa kune mafi yawan 'yan wuta". Sai suka ce: Dan me ya Manzon Allah? ya ce: "Kuna yawaita tsinuwa, kuma kuna butulcewa zamantakewa, banga masu tawayar hankali da Addini mafi tafiyar da hankalin namiji ba mai karfin niyya kamar ɗayanku ba - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
75. Waɗannan ciyawar suna mutuwa, kuma idan ɗayanku ya zo gidan wanka, to ya ce: Ina neman tsari ga Allah daga sharri da sharri
عربي Turanci urdu
76. Duk wanda ya ce a yayin da ya ji kiran sallah: (Ya Allah, Ma’abocin wannan cikakken kira da sallah da za'a tayar, Ka bai wa [Annabi] Muhammad al-Wasila da al-Fadila, kuma Ka tashe shi a matsayi abin yabo wanda Ka yi masa alƙawarin sa), ceto na zai halatta a gare shi ranar alƙiyama
عربي Turanci urdu
77. Kada ɗayanku ya kuskura ya yi sallah da tufa ɗaya, babu komai a kafaɗunsa
عربي Turanci urdu
78. Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka
عربي Turanci urdu
79. Na yi sallah tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya kasance yana yin sallama a damansa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah da albarkarSa", kuma a hagunsa: Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. "Aminci ya tabbata agare ku da rahamar Allah
عربي Turanci urdu
80. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni
عربي Turanci urdu
81. Alhasan da Alhusain su ne shugabannin matasan 'yan Aljanna
عربي Turanci urdu
82. Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya barin (raka'o'i) huɗu kafin azahar da raka’a biyu kafin sallar (Asuba)
عربي Turanci urdu
83. Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi
عربي Turanci urdu
84. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta {قل يأيها الكافرون} da {قل هو الله أحد} a raka'o'i biyu (kafin sallar) Asuba
عربي Turanci urdu
85. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ga wani mutum ya yi sallah shi kaɗai a bayan sawu, sai ya umarce shi ya sake sallar
عربي Turanci urdu
86. “Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyinta ba, to aurenta ɓatacce ne - sau uku - idan ya tare da ita, to sadakin ya kasance nata ne saboda abinda ya samu na (jima'i) daga gareta, idan suka yi jayayya to sarki (shi ne) waliyyin wanda ba shi da waliyyi
عربي Turanci urdu
87. Wanda ya zo wa matarsa ta duburarta tsinanne ne
عربي Turanci urdu
88. Allah ba Ya duba zuwa ga namijin da ya zo wa wani namiji ko wata mace ta dubura
عربي Turanci urdu
89. Na ce: Ya Manzon Allah, menene haƙƙin matar ɗayanmu a kansa?, ya ce; "Ka ciyar da ita idan kaci, ka tufatar da ita idan ka tufatar (da kanka), ko ka yi aiki, kada ka daki fuska, kada ka munana, kuma kada ka ƙaurace sai a ɗaki
عربي Turanci urdu
90. Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace
عربي Turanci urdu
91. Ku yaƙi mushrikai da dukiyoyinku da rayukanku da kuma harsunanku
عربي Turanci urdu
92. Mayafin musulmi zuwa rabin ƙwauri ne, kuma babu laifi - ko babu zunubi - a tsakanin sa da idan sawu, kuma abinda ya zama ƙasa da idan sawu to shi yana cikin wuta, wanda ya ja mayafinsa (ƙasa) dan girman kai to Allah ba zai yi duba zuwa gareshi ba
عربي Turanci urdu