kase kashen kana nan rassa

lis din Hadisai

1. Ku barni a abinda na bar muku, kaɗai waɗanda ke gabaninku sun halaka ne da tambayarsu da kuma saɓawarsu ga annabawansu
عربي Turanci urdu
2. Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
عربي Turanci urdu
3. Na hore ku da gaskiya, saboda gaskiya tana shiryarwa zuwa ga aikin alheri, kuma lallai aikin alheri yana shiryarwa zuwa ga Aljanna - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
4. Allah - Maɗaukakin sarki - Zai cewa mafi ƙanƙantar 'yan wuta azaba a ranar lahira: Shin da ace duk abinda ke cikin ƙasa naka ne shin zaka fanshi kanka da shi? Sai ya ce: Eh
عربي Turanci urdu
5. Manzon Allah SAW ya Kasance yana E'itikafi a cikin goman kowane Azumin Ramadan, to yayin da shekarar da aka karbi ransa ta zo yayi E'itikafi kwana Ashirin
عربي Turanci urdu
6. Wanda ya yi yaƙi dan kalmar Allah ta zama maɗaukakiya, to shi ne sabo da Allah
عربي Turanci urdu
7. Kar ku sanya alhariri (siririnsa) ko dibaji, kuma kar ku sha a cikin kofi na zinare ko na azurfa, haka nan kar ku ci a cikin farantansu, don kuwa na su ne (wanda ba muslmi) a nan duniya ku kuma zaku yi amfani da su a lahira
عربي Turanci urdu
8. Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku
عربي Turanci urdu
9. ku daidaita sahunku, don daidaita shahu na daga cikar sallah - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
10. Kada wani mumini ya ki wata mumina, in ya ki wata ɗabi’ar daga gareta to zai so wata ɗabi’ar daga gareta
عربي Turanci urdu
11. Idan kun zo wa bayan gida to kada ku fuskanci alƙibla, kuma kada ku juya mata baya sai dai ku fuskanci gabas ko ku fuskanci yamma
عربي Turanci urdu
12. Kada ɗayanku ya kuskura ya taɓa azzakarinsa da damansa, a halin yana fitsari, kuma kada ya yi tsarki na bayan gida da damansa, ko kuma ya yi nunfashi a ƙwarya
عربي Turanci urdu
13. Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana ɗaga hannayensa daura da kafaɗunsa in zai fara sallah,
عربي Turanci urdu
14. Ya Allah Ka nesanta tsakanina da kurakurai na kamar yadda Ka nesanta tsakanin mahudar rana da mafaɗarta
عربي Turanci urdu
15. Shin bana ba ku labari ba game da Jujal, wanda babu wani annabi da ya zantar da mutanensa shi ? lallai shi mai ido ɗaya ne, kuma shi zai zo a tare da shi akwai kwatankwacin aljanna da wuta,
عربي Turanci urdu
16. Ku daidaita a cikin sujjada, kar ku shimfida zira'oinku irin yadda kare ke shimfida nasa.
عربي Turanci urdu
17. Kaɗai kwatankwacin abokin zama na gari da mummunan abokin zama, kamar maɗaukin almiskine da mai busa zugazugi, - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
18. Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
19. Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana
عربي Turanci urdu
20. Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah
عربي Turanci urdu
21. ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amuransa alheri ne, kuma hakan ba ya kasancewa ga kowa sai ga mumini - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
22. SIFFAR WANKAN JANABA
عربي Turanci urdu
23. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance idan zai yi atishawa, yana sanya hannunsa - ko tufafinsa - a bakinsa, kuma ya runtse - ko matse - muryarsa da shi
عربي Turanci urdu
24. Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i
عربي Turanci urdu
25. Daga kanka ka fada za'a ji, ka roka a baka, ka nemi ceto za'a baka ceton
عربي Turanci urdu
26. Babu cuta mai yaɗuwa zuwa ga wani (da karantanta) babu canfi, ko mujiya, ko Safar, kuma ka guje wa kuturu kamar yadda kake guje wa zaki
عربي Turanci urdu
27. na rantse da Allah, Allah ya shiryar da mutum daya da kai shi ne mafi alheri daga jajayen ni'imomi (rakuma) - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
28. Lallai mutane idan suka ga azzalumi ba su yi riƙo da hannayensa ba, ya kusa Allah Ya gamesu da uƙuba daga gare shi
عربي Turanci urdu
29. Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi? - 6 ملاحظة
عربي Turanci urdu
30. Shin ba na baku labari da mafificin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a gurin Mamallakinku, mafi ɗaukakarsu a darajojinku
عربي Turanci urdu
31. ya rabauta idan gasgata hakan
عربي Turanci urdu
32. Mafificin yinin da rana ta ɓullo a cikinsa yinin Juma'a
عربي Turanci urdu
33. Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin, sannan Allah Ya turbuɗe hanacin" Aka ce: Wa ya Manzon Allah? Ya ce: "Wanda ya riski iyayen sa lokacin girma, ɗayan su ko su biyun amma bai shiga Aljanna ba
عربي Turanci urdu
34. Masu kaɗaitawa sun rigaya
عربي Turanci urdu
35. Na umarce ka da yawan sujjada ga Allah, domin kai ba za ka yi wata sujjada ga Allah ba, sai Allah Ya ɗaga darajar ka da ita, kuma Ya sarayar da kuskure da ita
عربي Turanci urdu
36. Wanda ya sallaci sanyaya biyu zai shiga aljanna - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
37. Idan aka tambayi musulmi a cikin ƙabari: Yana shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad manzon Allah ne
عربي Turanci urdu
38. "Lallai Allah ya yafewa Al-umma ta Kuskure da Mantuwa, da kuma abunda aka Tilasta musu akansa" - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
39. Ku ji tsoron Allah a duk inda kuke, kuma ku bi munanan abubuwa masu kyau, ku share su, ku ƙirƙira mutane da kyawawan halaye - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
40. Lalle ne Allah - Maɗaukakin sarki - Yana shimfiɗa hannunSa da daddare domin mai laifi da rana ya tuba, kuma Yana shimfiɗa hannunSa da rana domin mai laifi da daddare ya tuba, har sai rana ta ɓullo daga yammacinta - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
41. Kowacce gaɓa daga (jikin) mutane akwai sadaka a kanta
عربي Turanci urdu
42. Jinin Mutum Musulmi Bai halatta basai da dayan abubuwa Uku : Tsoho Mazinaci , ko wanda ya kashe a kashe shi, Da Mutumin da yayi Ridda daga Addininsa ya futa daga cikin Musulmi.
عربي Turanci urdu
43. Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
44. Zalunci duhu ne a ranar tashin kiyama - 3 ملاحظة
عربي Turanci urdu
45. Wanda ya yi wanka irin wankan janaba a ranar Juma`a, sannan ya tafi, kamar ya bayar da sadakar rakuma ne
عربي Turanci urdu
46. Wanda ya ci abin ci sai ya ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ciyar da ni wannan kuma Ya azirtani shi ba tare da wata dabara daga gareni ko ƙarfi ba, za'a gafarta masa abinda ya gabata daga zunubinsa
عربي Turanci urdu
47. Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwala sannan ya zo Juma'a sai ya saurari huduba kuma ya yi shiru za'a gafarta masa abinda ke tsakaninsa da tsakanin Juma'a da ƙarin kwanaki uku
عربي Turanci urdu
48. Yakai ɗan Adam lallai cewa kai baka roƙeni ba, ka yi kwaɗayi gareni zan gafarta maka abinda ya kasance gareka babu ruwaNa - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
49. Ya ku mutane ku yaɗa sallama, ku ciyar da abinci, ku sadar da zumunci, ku yi sallah alhali mutane suna bacci, zaku shiga aljanna cikin aminci
عربي Turanci urdu
50. Lallai Addini mai sauƙi ne, babu wanda zai tsananta cikinsa face sai ya rinjaye shi, saboda haka ku daidaita ku kusanto
عربي Turanci urdu
51. An tambayi Annabi game da abu mafi yawa da yake shigar da Mutane" Al-janna? ya ce: Tsoron Allah da kyawawan Halaye, kuma aka tambaye shi game da abu mafi yawa da yake jefa Mutane wuta sai ya ce Baki da Farjin su"
عربي Turanci urdu
52. Duk wanda yake da iko a cikinku to ya yi aure, domin cewa shi ne yafi rintse ido, kuma ya fi katange farji, wanda ba zai iya ba to na umarce shi da azimi, domin shi kariyane gare shi
عربي Turanci urdu
53. "Mutane Uku ba zasu shiga Al-janna ba: Mashayin giya da mai yanke Zumunci, da Mai Gasgata Masu Sihiri" - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
54. Kuma ai ansanya Limami ne don ayi koyi da shi, to kuma kada ku saba Masa, to idan yayi kabbara to kuyi kabbara, kuma idan yayi ruku'u to kuyi ruku'i, kuma idan yace Allah yaji mai gode masa,to ku ce: Ubangijinmu godiya ta tabbata a gareka, kuma idan yayi Sujada to kuyi Sujada, kuma idan yai Sallah a zaune to kuyi sallah kuma a a zaune baki dayanku
عربي Turanci urdu
55. Shin bana shiryar daku ga mafi alheri daga abinda kuka tambaya ba? idan kun kwanta - ko kunzo shinfiɗarku - to ku yi tasbihi sau talatin da uku, ku yi hamdala sau talatin da uku, ku yi kabbara sau talatin da da hudu, to shi ne mafi alheri gareku daga dan aiki
عربي Turanci urdu
56. "wani Mutum yace: Ya Manzon Allah wani Mutum daga cikin mu yakan gamu da Danuwansa ko Abokinsa shin ya durkusa masa, sai ya ce to ya rikeshi ya ya sunbance shi ? sai yace aa sai ya ce to ya kama hannunsa su gaisa? ya ce: Ey" - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
57. Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance mafi kyauta cikin mutane, kuma ya kasance mafi kyutar da yake yi a Ramadan ne lokacin da Jibril ya haɗu da shi
عربي Turanci urdu
58. Wanda ya rantse sai ya ce a cikin rantsuwarsa: Na rantse da Lata da Uzza, to ya ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, wanda ya ce wa abokinsa: Zo mu yi caca tare, to ya yi sadaka
عربي Turanci urdu
59. Shin kun san waye muflis (wanda aka yi wa wasoso)? - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
60. ‘’Babu wani daga cikinku face sai Allah ya yi magana da shi, babu wani tafinta a tsakaninsu
عربي Turanci urdu
61. Ya kai Ruwaifia,watakila rayuwarka tayi tsawo, saboda haka bawa Mutane labarin cewa duk wanda ya daure gemunsa, ko ya daura tsirkiya, ko yayi tsarki turoson dabbobi ko kashi, to babu shi babu Annabi Muhammad
عربي Turanci urdu
62. Wanda ya zantar da wani Hadisi daga gareni yana ganin cewa shi ƙarya ne to shi yana ɗaya daga cikin maƙaryata - 4 ملاحظة
عربي Turanci urdu
63. ya kasance idan ya shiga masallaci sai ya ce: "Ina neman tsarin Allah Mai girma, da fuskarSa Mai girma, da sarautarSa daɗaɗɗiya, daga Shaiɗan abin jefewa
عربي Turanci urdu
64. Lallai Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Zai cewa 'yan aljanna: Yaku 'yan aljanna? sai su ce: AmsawarKa ya Ubangijinmu da dai amsawarKa, sai Ya ce: Shin kun yarda? Sai su ce: Dan me ba zamu yarda ba alhali Ka bamu abinda baKa bawa wani daga halittarKa ba?
عربي Turanci urdu
65. Lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Al-wala sai ya yi Alwala sai ya kuskure bakinsa, sannan ya face, sannan ya wanke fuskarsa sau Uku,da hannunsa na Dama sau Uku, xayanma sau uku, kuma ya shafi kansa da Ruwa ba na ragowar hannunsa ba, kuma ya wanke Qafarsa har ya tsaftace ta - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
66. Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana wanka, ko ya kasance yana wanka, da sa'i zuwa mudu biyar, kuma yana alwala da mudu
عربي Turanci urdu
67. Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
68. Mala'iku ba sa shiga gidan da yake akwai kare ko hoto a cikinsa
عربي Turanci urdu
69. Kada ku yi rantsuwa da ɗagutai, ko da iyayenku
عربي Turanci urdu
70. Duk wanda yayi alwala ranar juma'a zai samu lafiya, kuma duk wanda yayi alwala shine mafi alkhairi - 1 ملاحظة
عربي Turanci urdu
71. Idan ranar Juma'a mala'iku suka tsaya a kofar masallacin, sun rubuta na farko, sannan na farko
عربي Turanci urdu
72. Kada ku zagi sahabbaina, da a ce ɗayanku zai ciyar da zinare kwatankwacin dutsen Uhudu ba zai kai cikin mudun ɗayansu ba, ko rabinsa
عربي Turanci urdu
73. Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su
عربي Turanci urdu
74. 'Lallai waɗannan sallolin biyu sune mafi nauyin salloli akan munafuki, da kun san abinda ke cikinsu da kun zo musu koda da jan ciki ne akan gwiwowi
عربي Turanci urdu
75. Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba
عربي Turanci urdu
76. Idan Ramadan ya zo to ki yi umara, domin umara a cikinsa yana daidai da Hajji - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu
77. Ya manzon Allah, muna ganin yaƙi shi ne mafificin aiki, shin ba ma yi yaƙi ba? ya ce: "A'a, sai dai mafificin yaƙi: Shi ne kubutaccen aikin Hajji
عربي Turanci urdu
78. Na kasance tare da annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya kai zuwa jujin wasu mutane, sai ya yi fitsari a tsaye,
عربي Turanci urdu
79. Kada ku yi hassada, kuma kada ku yi cinikin koɗe (shi ne wani ya zo sayan wani abu sai wani a kasuwar wanda ba ya nufin sayan sai ya zo ya ce a siyar mini a kaza sai ya faɗi sama da kuɗin kayan), kuma kada ku yi gaba, kada ku juyawa juna baya, kuma kada wani ya yi ciniki akan cinikin wani, ku zama bayin Allah 'yan uwan juna - 2 ملاحظة
عربي Turanci urdu