عن المِقدام بن معدي كرب رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«إِذَا أَحَبَّ الرَّجُلُ أَخَاهُ فَلْيُخْبِرْهُ أَنَّهُ يُحِبُّهُ».

[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 5124]
المزيــد ...

Daga Mikdam dan Ma'adikarib - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa".

[Ingantacce ne] - [Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i a cikin alkubra haka Ahmad suka ruwaito shi] - [Sunan Abi Dawud - 5124]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana daya daga sabubban da suke karfafa alaka tsakanin muminai kuma suke yada soyayya a tsakaninsu, shi ne cewa idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana son sa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Falalar tsarkakakkiyar soyayya saboda Allah - Madaukakin sarki - ba dan maslaha ta duniya ba.
  2. Anso sanadar da wanda ake so sabo da Allah da soyayyrsa, dan soyayya da kauna su karu.
  3. Yada soyayya tsakanin muminai yana karfafa 'yan uwantaka ta imani, kuma yana kiyaye zamantakewa daga rarrabuwa.
Manufofin Fassarorin
Yare: Turanci urdu Sifaniyanci Kari (67)