عن أبي هريرة رضي الله عنه قال:
سُئِلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ الْجَنَّةَ، فَقَالَ: «تَقْوَى اللهِ وَحُسْنُ الْخُلُقِ»، وَسُئِلَ عَنْ أَكْثَرِ مَا يُدْخِلُ النَّاسَ النَّارَ فَقَالَ: «الْفَمُ وَالْفَرْجُ».
[حسن صحيح] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 2004]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane aljanna, sai ya ce: "Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u", kuma an tambayeshi game da mafi yawan abin da yake shigar da mutane wuta sai ya ce: "Baki da farji".
[Hasan ne kuma Ingantacce] - - [سنن الترمذي - 2004]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a greshi - yana bayyana cewa mafi giman sabubban da suke shigar da mutane aljanna sabubba biyu ne, sune:
Tsoron Allah da kyawawan ɗabi'u.
Tsoron Allah: Shi ne ka sanya kariya tsakaninka da tsakanin azabar Allah, ta hanyar aikata umarninsa da nisantar hane-hanensa.
Kyakkyawar ɗabi'a: Tana kasancewa ne da shinfiɗar fuska, da yin aikin kirki, da kamewa daga cuta.
Kuma mafi girman sabubban da suke shigarwa wuta sabubba biyu ne, su ne:
Harshe da farji.
yana daga saɓon harshe: Ƙarya, da raɗa, da annamimanci da wasunsu.
Yana daga saɓon farji: Zina da luwaɗi da wasunsu.