عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«كان رجلٌ يُدَايِنُ الناسَ، فكان يقول لفتاه: إذا أتيتَ مُعسِرًا فتجاوز عنه، لعل اللهَ يَتجاوزُ عنا، فلقي اللهَ فتجاوز عنه».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 1562]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Wani mutum ya kasance yana bawa mutane bashi, ya kasance yana cewa wani yaronsa: Idan kaje wurin wanda ke cikin muwuyacin hali to ka kau da kai gare shi , muna fatan Allah ya ketare mana (zunubanmu), sai ya gamu da Allah sai Ya yafe masa".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1562]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari: Game da mutumin da ya kasance yana mu'amalar bashi tare da mutane, ko ya siyar bashi, Ya kasance yana cewa yaronsa wanda yake karbo masa basukan dake hannun mutane: Idan ka je wurin wanda ake bi bashi kuma ba shi da abinda zai biya bashin dake kansa dan gajiyawarsa "To ka kau da kai gare shi"; ko dai da jinkirta masa da rashin nace masa a kan ya biya., Ko da karbar abinda ke tare da shi koda tare da abinda ke cikinsa ne na tawaya, hakan dan kwadayi daga gare shi akan Allah Ya ketare masa kuma ya yi masa rangwame. Lokacin da ya mutu sai Allah ya yi masa afuwa kuma ya ketare daga munanan ayyukansa.