عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم كان يقول:
«الصَّلَوَاتُ الْخَمْسُ، وَالْجُمُعَةُ إِلَى الْجُمُعَةِ، وَرَمَضَانُ إِلَى رَمَضَانَ، مُكَفِّرَاتٌ مَا بَيْنَهُنَّ إِذَا اجْتَنَبَ الْكَبَائِرَ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 233]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce
"Salloli biyar, da Juma'a zuwa Juma'a, da Ramadan zuwa Ramadan, masu kankare a binda ke tsakaninsu ne idan ya nisanci manyan zunubai".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 233]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa; Salloli biyar ababen faralantawa a yini da dare ne, da sallar Juma'a a kowane mako, da azimin watan Ramadan a kowacce shekara, masu kankare abinda ke tsakaninsu ne na kananan zunubai da sharadin nisantar manyan zunubai. Amma manyan zunubai kamar zina da shan giya ba mai kankaresu sai tuba.