عن المقدام بن معدِيْكَرِب رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«أَلَا هَلْ عَسَى رَجُلٌ يَبْلُغُهُ الْحَدِيثُ عَنِّي وَهُوَ مُتَّكِئٌ عَلَى أَرِيكَتِهِ فَيَقُولُ: بَيْنَنَا وَبَيْنَكُمْ كِتَابُ اللهِ، فَمَا وَجَدْنَا فِيهِ حَلَالًا اسْتَحْلَلْنَاهُ، وَمَا وَجَدْنَا فِيهِ حَرَامًا حَرَّمْنَاهُ، وَإِنَّ مَا حَرَّمَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَمَا حَرَّمَ اللهُ».
[صحيح] - [رواه أبو داود والترمذي وابن ماجه] - [سنن الترمذي: 2664]
المزيــد ...
Daga Mikdam dan Maadikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - ya ce
"Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane".
[Ingantacce ne] - - [سنن الترمذي - 2664]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.