عن جرير بن عبد الله رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ لَا يَرْحَمِ النَّاسَ لَا يَرْحَمْهُ اللهُ عَزَّ وَجَلَّ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 2319]
المزيــد ...
Daga Jariri ɗan Abbdullah - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon - Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2319]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa wanda baya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba, to, jin ƙan bawa ga halitta yana daga mafi girman sabubban da ake samun rahamar Allah da su.