عن أبي هريرة رضي الله عنه أن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«لَيْسَ الشَّدِيدُ بِالصُّرَعَةِ، إِنَّمَا الشَّدِيدُ الَّذِي يَمْلِكُ نَفْسَهُ عِنْدَ الْغَضَبِ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 6114]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ce:
"Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6114]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa ƙarfi na haƙiƙa ba ƙarfin jiki ba ne, ko wanda yake ka da wasu ƙarfafa, kaɗai mai tsananin ƙarfi shi ne wanda yake yaƙar zuciyarsa, kuma yake rinjayarta a lokacin da fushi ya yi tsanani a gareshi; domin cewa wannan yana nuni a kan ƙarfin da zai tabbatar da shi a kan kansa da rinjayarsa a kan Shaiɗan.