+ -

عن أبي هريرة رضي الله عنه عن رسول الله صلى الله عليه وسلم قال:
«مَا نَقَصَتْ صَدَقَةٌ مِنْ مَالٍ، وَمَا زَادَ اللهُ عَبْدًا بِعَفْوٍ إِلَّا عِزًّا، وَمَا تَوَاضَعَ أَحَدٌ لِلهِ إِلَّا رَفَعَهُ اللهُ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2588]
المزيــد ...

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Sadaka ba ta rage dukiya, kuma Allah ba Ya ƙarawa bawa komai da afuwa sai ɗaukaka, ba wanda zai yi tawalu'i ga Allah sai Allah Ya ɗaukaka shi".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2588]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa sadaka ba ta rage dukiya, kai! tana tunkuɗe masa illoli, kuma Allah Yana musanyawa mai ita da alheri mai girma, sai ta zama ƙari ba ragi ba.
Kuma afuwa tare da iko a kan ramuwa ko kama (mai laifin), ba sa karawa mai yinsu komai sai ƙarfi da buwaya.
Kuma wani ba zai ƙanƙan da kai, ya ƙasƙanta ga Allah ba, ba don tsoron wani ba, ba don yaudara (na nuna tausayi) gareshi ba, ba don neman wani abin amfani daga wajensa ba, sai sakamkonsa ya zama ɗaukaka ne da sharafi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Alheri da rabauta (suna ) cikin kamanta shari'a da aikata alheri ko da wasu daga mutane sun yi zaton cewa saɓanin hakan ne.