عن عبد الله بن عمرو رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«يقالُ لصاحبِ القرآن: اقرَأ وارتَقِ، ورتِّل كما كُنْتَ ترتِّل في الدُنيا، فإن منزِلَكَ عندَ آخرِ آية تقرؤها».
[حسن] - [رواه أبو داود والترمذي والنسائي في الكبرى وأحمد] - [سنن أبي داود: 1464]
المزيــد ...
Daga Abdullahi dan Amr dan Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
"Za'a ce da ma'abocin Alkur’ani: Karanta ka daukaka, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya, domin cewa matsayinka zai tasayane a karshen ayar da ka karantata".
[Hasan ne] - - [سنن أبي داود - 1464]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa, za’a ce da makarancin Alkur’ani, mai aiki da abinda ke cikinsa, wanda ya lazimceshi a karatu da hadda idan ya shiga Aljanna: Ka karanta ka daukaka da wannan a cikin darajojin Aljanna, ka rera kamar yadda ka kasance kana rerawa a duniya da karanta shi da bi ahankali da nutsuwa; domin cewa matsayinka na karshen ayar da ka karantata ne.