عن عثمان بن عفان رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«مَنْ تَوَضَّأَ فَأَحْسَنَ الْوُضُوءَ خَرَجَتْ خَطَايَاهُ مِنْ جَسَدِهِ حَتَّى تَخْرُجَ مِنْ تَحْتِ أَظْفَارِهِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 245]
المزيــد ...
Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 245]
Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi yana ba da labari cewa wanda ya yi alwala tare da kula da sunnonita da ladubbanta, to, hakan zai kasance daga sababi na kankare laifuka, da share kukurai, har sai zunubansa sun fita ta ƙarƙashin farcensa na hannu da ƙafa.