عن أبِي هُرَيرةَ رضي الله عنه أنَّ رسول الله صلى الله عليه وسلمَ قال:
«إذا قُلْتَ لِصَاحِبِكَ: أَنْصِتْ، يومَ الجمعةِ، والْإِمامُ يَخْطُبُ، فَقَدْ لَغَوْتَ».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 851]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:
"Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 851]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa daga ladubba na wajibi ga wanda ya halarci huɗubar Juma'a: Shi ne yin ahieu ga mai huɗuba; don ya yi tuntuntuni cikin wa'azin, kuma wanda ya yi magana - ko da da ƙanƙanin abu ne - alhali liman yana huɗuba, sai ya ce wa waninsa: "Ka yi shiru" ka "saurara", to, haƙiƙa falalar sallar Juma'a ta wuce shi.