عَنْ مُعَاذٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ:
كُنْتُ رِدْفَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَلَى حِمَارٍ يُقَالُ لَهُ عُفَيْرٌ، فَقَالَ: «يَا مُعَاذُ، هَلْ تَدْرِي حَقَّ اللَّهِ عَلَى عِبَادِهِ، وَمَا حَقُّ العِبَادِ عَلَى اللَّهِ؟»، قُلْتُ: اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَعْلَمُ، قَالَ: «فَإِنَّ حَقَّ اللَّهِ عَلَى العِبَادِ أَنْ يَعْبُدُوهُ وَلا يُشْرِكُوا بِهِ شَيْئًا، وَحَقَّ العِبَادِ عَلَى اللَّهِ أَنْ لا يُعَذِّبَ مَنْ لا يُشْرِكُ بِهِ شَيْئًا»، فَقُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ أَفَلاَ أُبَشِّرُ بِهِ النَّاسَ؟ قَالَ: «لا تُبَشِّرْهُمْ، فَيَتَّكِلُوا».
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 2856]
المزيــد ...
Daga Mu'az - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Na kasance a bayan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan wani jaki ana ce masa Ufair, sai ya ce: "Ya Mu'az, shin kasan hakkin Allah akan bayin Sa, kuma menene hakkin bayi ga Allah?", sai na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani, ya ce: "Lalle cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa kada su hada shi komai, hakkin bayi ga Allah ba zai azabtar da wanda bai tarayya daShi da komaiba", sai na ce: Ya Manzon Allah shin ba nayiwa mutane albishir da shi ba? Ya ce: "Kada ka yi musu albishir, sai su dogara".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2856]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.