عن جَرِيْر بنِ عبدِ الله رضي الله عنه قال:
كُنَّا عِنْدَ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَنَظَرَ إِلَى الْقَمَرِ لَيْلَةً -يَعْنِي الْبَدْرَ- فَقَالَ: «إِنَّكُمْ سَتَرَوْنَ رَبَّكُمْ كَمَا تَرَوْنَ هَذَا الْقَمَرَ، لَا تُضَامُونَ فِي رُؤْيَتِهِ، فَإِنِ اسْتَطَعْتُمْ أَنْ لَا تُغْلَبُوا عَلَى صَلَاةٍ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ غُرُوبِهَا فَافْعَلُوا» ثُمَّ قَرَأَ: «{وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ قَبْلَ طُلُوعِ الشَّمْسِ وَقَبْلَ الْغُرُوبِ}»
[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح البخاري: 554]
المزيــد ...
Daga Jariri dan Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce:
Mun kasance a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya dubi wata a wani dare - yana nufin daren haske -(daran sha hudu ga wata) sai Ya ce: "Lallai cewa ku zaku ga Ubanugijinku kamar yadda kuke ganin wannan watan, ba zaku wahala ba a ganinsa, idan zaku iya kokarin kada a rinjayeku akan sallarku kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta to ku aikata" sannan ya karanta: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kuma kafin faduwarta}".
[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح البخاري - 554]
Sahabbai sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare sai ya dubi wata - daren goma sha hudu -, sai ya ce: Lallai muminai za su ga Ubanbijinsu a hakika da ido ba tare da wani rikici ba, kuma cewa su ba za su yi cunkoso ba, kuma wahala ba zata samesu ba ko tsanani a yayin ganinsa - Madaukakin sarki -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kuna da ikon yanke abubuwan da zasu hana ku sallar Asuba da sallar La'asar to ku aikata, ku zo da su (Sallolin) a cike a lokacinsu a cikin jama'a, domin cewa hakan yana daga sabubban gani zuwa fuskar Allah - Mai girma da daukaka -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta ayar: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kafin faduwarta}.