عن أبي هريرة رضي الله عنه عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«لَيْسَ شَيْءٌ أَكْرَمَ عَلَى اللهِ تَعَالَى مِنَ الدُّعَاءِ».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد] - [سنن الترمذي: 3370]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce:
"Babu wani abu mafi girma a wurin Allah - Maɗaukakin sarki- sama da addu'a".
[Hasan ne] - - [سنن الترمذي - 3370]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa babu wani abu a ibadu mafifici a wurin Allah sama da addu'a; domin a cikinta akwai iƙirari da wadatar Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -, da kuma iƙirari da gajiyawar bawa da buƙatuwarsa gareshi.