+ -

عَنْ جُوَيْرِيَةَ أُمِّ المؤْمنينَ رَضيَ اللهُ عنها:
أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَرَجَ مِنْ عِنْدِهَا بُكْرَةً حِينَ صَلَّى الصُّبْحَ، وَهِيَ فِي مَسْجِدِهَا، ثُمَّ رَجَعَ بَعْدَ أَنْ أَضْحَى، وَهِيَ جَالِسَةٌ، فَقَالَ: «مَا زِلْتِ عَلَى الْحَالِ الَّتِي فَارَقْتُكِ عَلَيْهَا؟» قَالَتْ: نَعَمْ، قَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «لَقَدْ قُلْتُ بَعْدَكِ أَرْبَعَ كَلِمَاتٍ، ثَلَاثَ مَرَّاتٍ، لَوْ وُزِنَتْ بِمَا قُلْتِ مُنْذُ الْيَوْمِ لَوَزَنَتْهُنَّ: سُبْحَانَ اللهِ وَبِحَمْدِهِ، عَدَدَ خَلْقِهِ وَرِضَا نَفْسِهِ وَزِنَةَ عَرْشِهِ وَمِدَادَ كَلِمَاتِهِ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2726]
المزيــد ...

Daga Nana Juwairiyya Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita -:
Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya fita daga wurinta da sassafe yayin da ya yi sallar Asuba, alhali tana wurin sallarta, sannan ya dawo bayan hantsi ya daga, alhali tana nan a zaune, sai ya ce: «Ba ki gusheba a kan halin da na barki a kansa?» Ta ce: Eh, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: «Haƙiƙa na faɗi wasu kalmomi huɗu a bayanki, sau uku, da za'a auna su da abin da kika faɗa a yau da sun rinjaye su: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyar Sa, adadin halittar Sa, da yardar kanSa, da nauyin Al’Arshin Sa, da tawadar kalmomin Sa).

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2726]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fita daga wurin matarsa Uwar muminai Nana Juwairiyya - Allah Ya yarda da ita - a farkon yini lokacin da ya yi sallar Asuba, alhali ita tana zaune a wurin sallarta, sannan ya dawo bayan rana ta ɗaga lokacin sallar walaha, alhali ita ba ta gushe ba tana zaune a wurinta, sai ya ce: Shin baki gushe ba akan halin da na barki akansa? Ta ce: Eh, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Haƙiƙa a bayanki na faɗi wasu kalmomi huɗu, kuma na maimaita su sau uku, da za'a auna da abinda kika faɗa a gaba ɗayan lokacin da kike a zaune a cikinsa da sun rinjaye su: (Tsarki ya tabbata ga Allah) da tsarkakarSa daga dukkan tawaya, (da godiyarSa) inda Yake da kyakkyawan yabon da Ya shiryar ga hakan, (adadin halittarSa) waɗanda babu mai iya iyakancesu sai Allah, (da yardar kanSa) da gwargwadan abinda Ya yardar maSa ga wanda Allah Ya yarda da shi daga bayinSa kuma shi wani abu ne ba’a kewaye shi da sani , (da awon Al’arshin sa) wanda shi ne mafi girman halittu kuma mafi nauyinsu, (da tawadar kalmominSa) kuma kalmomin Allah ba sa taƙaituwa kuma ba sa ƙarewa; wannan yana gemawa kuma yana ƙunsar rabe-raben uku; domin tawadar kalmominSa - tsarki ya tabbatar maSa - babu karewa ga iyakarta, ko ga siffarSa ko ga adaddinsa, sai dai abin nufi: Kai matuka da shi a yawa; domin a farko ya ambaci abinda kirge mai yawa na adadin halitta yake iyakance shi , sannan ya hau zuwa abinda shi ne mafi girma daga nan kuma ya bayyanar daga gare shi da yardar kanSa, sannan awon mafi girman halittu shi ne al'Arshi; na farkon dan kirgawa ne da kuma yawa, na biyun kuma da siffa ne da kuma kaifiyya, na uku dan girma da kuma nauyi.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Swahili Asami الأمهرية الهولندية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Bayanin falalar waɗannan kalmomin, da kuma kwaɗaitarwa akan faɗinsu.
  2. Zikiri yana fifita, sashinsa ya fi sashi.
  3. Nawawi ya faɗa akan faɗinsa (tsarki ya tabbatarwa Allah da godiyrSa tawadar kalmominSa): Abin nufi shi ne kai matuƙa da shi a cikin yawa; domin cewa shi a farko ya ambaci abinda ƙididdiga mai yawa take iyakance shi na adadin halitta, sannan awon al’Arshi, sannan ya hau zuwa abinda shi ne mafi girma daga hakan kuma ya bayyanar game da shi da wannan, wato abinda ƙididdiga bata iya iyakance shi kama yanda ba'a iya iyakance ta.
  4. Ibnul Kayyima ya ce: Abinda yake tsayuwa da zuciyar mai zikiri lokacin da yake cewa: Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarSa, adadin halittarSa... har zuwa ƙarshensa na saninSa da tsarkakeShi da kuma girmamaShi daga wannan gwargwadan abin ambata daga adadin shi ne mafi girma daga abinda yake tsayuwa da zuciyar mai faɗin: "Tsarki ya tabbata ga Allah" kawai.
  5. Shiryarwa zuwa kalmomi masu tattarowa waɗanda suke ɗaukar lafuzza kaɗan, kuma akansu a bada falala mai yawa da kuma sakamako.