عن أبي هريرة رضي الله عنه مرفوعاً: «ليس شيءٌ أكرمَ على الله من الدعاء».
[حسن] - [رواه الترمذي وابن ماجه وأحمد]
المزيــد ...
An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu abunda yafi girma wajen Allah kamar Addu'a"
[Hasan ne] - [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]
Babu abunda yafi yafi girma wajen Allah kamar Addu'a) Sabida ita Ibada ce, Kuma ita Ibada ita Allah ya halicci bayi sabida ita, Saboda Addu'a tana nuna ikon Allah da kuma yalwar Iliminsa, da kuma gajiyawar Mai rokon da bukatuwarsa, saboda wannan Addu'a ta zama Mafi girman Abubuwa a wajen Allah maigirma da daukaka.