+ -

عن عبد الله بن عمر رضي الله عنهما قال:
سَمِعَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ رَجُلًا يَعِظُ أَخَاهُ فِي الْحَيَاءِ، فَقَالَ: «الْحَيَاءُ مِنَ الْإِيمَانِ».

[صحيح] - [متفق عليه] - [صحيح مسلم: 36]
المزيــد ...

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".

[Ingantacce ne] - [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi] - [صحيح مسلم - 36]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wani mutum yana yi wa wani ɗan uwansa nasihar cewa ya bar yawan kunya! sai ya bayyana masa cewa kunya tana daga imani, kuma ba ta zuwa sai da alheri.
Kunya ɗabi'a ce da take sa aikata mai kyau da barin mummuna.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Abin da zai hana ka alheri ba a ambatonsa kunya, kai ana ambatonsa tsoro da gajiyawa da rauni da ragonta.
  2. Kunyar Allah - Mai girma da daukaka - tana kasancewa ne da aikata abubuwan da aka umarta, da barin abubuwan da aka hana.
  3. Kunyar ababen halitta tana kasancewa ne da girmamasu, da saukar da su masaukansu, da nisantar abin da zai munana a al'adance.