+ -

عن سَمُرَة بن جندبٍ رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«أَحَبُّ الْكَلَامِ إِلَى اللهِ أَرْبَعٌ: سُبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْدُ لِلهِ، وَلَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، وَاللهُ أَكْبَرُ، لَا يَضُرُّكَ بِأَيِّهِنَّ بَدَأْتَ».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2137]
المزيــد ...

Daga Samura ɗan Jundub - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gagreshi - ya ce:
"Mafi soyuwar zance ga Allah huɗu ne: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne mafi girma, da kowanne ka fara daga cikinsu ba ya cutar da kai".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2137]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi soyuwar zance a wurin Allah huɗu ne:
Tsarki ya tabbata ga Allah; Tana nufin tsarkake Allah - Maɗaukakin sarki - daga kowace tawaya.
Godiya ta tabbata ga Allah: Siffanta Allah ne da cikakkiyar cika tare da soyayyarSa da girmamashi.
Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah: Wato; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.
Allah ne mafi girma: Wato; Mafi girma kuma Mafi buwaya daga dukkan komai.
Kuma cewa falalarta da samun ladanta ba ya nufin sai lallai an jeranta su a yayin furuci da su.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية Oromo Kanadische Übersetzung Aserbaidschanisch الأوزبكية الأوكرانية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Sauƙin shari'a, ta inda ba ya cutarwa da kowaccen waɗannan kalmomin ka fara.