عن أبي مسعود الأنصاري رضي الله عنه قال:
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: إِنِّي أُبْدِعَ بِي فَاحْمِلْنِي، فَقَالَ: «مَا عِنْدِي»، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَدُلُّهُ عَلَى مَنْ يَحْمِلُهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 1893]
المزيــد ...
Daga Abu Mas'ud Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 1893]
Wani mutum ya zo ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Lallai cewa dabbata ta halaka, ka ɗorani a kan wata dabbar, kuma ka ba ni wani abin hawan da zai kai ni, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba shi uzuri cewa ba shi da wani abin da zai dorashi a kansa, sai wani mutum da ya ke wurin ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa ya zama abokin tarayyar mai sadakar a lada; domin ya shiryar da mabuƙacin zuwa gareshi.