+ -

عن أبي موسى الأشعري رضي الله عنه قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم:
«إِذَا مَرِضَ الْعَبْدُ أَوْ سَافَرَ كُتِبَ لَهُ مِثْلُ مَا كَانَ يَعْمَلُ مُقِيمًا صَحِيحًا».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 2996]
المزيــد ...

Daga Abu Musa Al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Idan bawa yayi rashin lafiya ko yayi tafiya za'a rubuta masa tamkar abinda ya kasance yana aikatawa alhali yana zaman gida kuma lafiyayye".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 2996]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bada labari game da falalar Allah da rahamarSa, kuma cewa musulmi idan ya kasance al'adarsa cewa yana aikata wani aiki na gari a halin lafiyarsa da kuma zaman gidansa, sannan wani uzuri ya faru da shi sai ya yi rashin lafiya bai samu damar yin sa ba, ko ya shagalta da tafiya bai samu ya yi shi ba, ko wani uzurin; to cewa shi za'a rubuta masa lada cikakke, kamar da ya aikata shi a halin lafiya da zaman gida.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy الفولانية Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch الأكانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Yalwal falalar Allah ga bayinSa.
  2. Kwadaitarwa akan kokari a biyayya da cin ribar lokuta a halin lafiya da faraga.