+ -

عَنِ ابْنِ عُمَرَ رضي الله عنهما عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، قَالَ:
«مَثَلُ الْمُنَافِقِ، كَمَثَلِ الشَّاةِ الْعَائِرَةِ بَيْنَ الْغَنَمَيْنِ تَعِيرُ إِلَى هَذِهِ مَرَّةً وَإِلَى هَذِهِ مَرَّةً».

[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 2784]
المزيــد ...

Daga Dan Umar - Allah Ya yarda da su - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:
'Misalin munafiki, kamar akuya ce mai kaikawo tsakanin turke biyu, tana kaikawo gurin wadannan wani lokaci da kuma zuwa wadancan a wani lokacin".

[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 2784]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية الطاجيكية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف البلغارية Aserbaidschanisch اليونانية الأوزبكية الأوكرانية الجورجية اللينجالا المقدونية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Daga shiryarwar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - buga misali dan kusanto da ma'anoni.
  2. Bayanin halin munafikai na kaikawo da kokwanto da rashin tabbas.
  3. Gargadi akan halin munafikai, da kwadaitarwa akan gaskiya da kudirin niyya a kan imani a zahiri da badini.