عن أبي هريرة رضي الله عنه:
أَنَّ رَجُلًا قَالَ لِلنَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: أَوْصِنِي، قَالَ: «لَا تَغْضَبْ» فَرَدَّدَ مِرَارًا قَالَ: «لَا تَغْضَبْ».
[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6116]
المزيــد ...
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
"Lallai cewa wani mutum ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Yi min wasiyya, sai ya ce: "Kada ka yi fushi" sai ya maimata da yawa, ya ce: "Kada ka yi fushi".
[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6116]
Ɗaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da zai amfaneshi, sai ya umarceshi da kada ya yi fushi, ma'anar hakan cewa shi ne ya nisanci sabubban da za su sa shi fushi, kuma ya tsare kansa idan fushi ya faru gareshi, kada ya zarce tare da fushinsa da kisa ko duka ko zagi da makamancin hakan.
Mutumin ya maimaita neman wasiyya da yawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai ƙara komai a wasiyyarsa ba a kan "Kada ka yi fushi".