+ -

عن عبد الله بن عمرو بن العاص رضي الله عنهما عن النبي صلى الله عليه وسلم قال:
«الْكَبَائِرُ: الْإِشْرَاكُ بِاللهِ، وَعُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ، وَقَتْلُ النَّفْسِ، وَالْيَمِينُ الْغَمُوسُ».

[صحيح] - [رواه البخاري] - [صحيح البخاري: 6675]
المزيــد ...

Daga Abdullahi Dan Amr Dan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:
"Manyan zanubai su ne: Yi wa Allah shirka, da saɓawa iyaye, da kashe rai, rantsuwa mai dulmiyarwa".

[Ingantacce ne] - [Buhari ne ya rawaito shi] - [صحيح البخاري - 6675]

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana manyan zunubai cewa su ne waɗanda aka yi narko (alƙawarin azaba) a kan wanda ya aikata su da narko mai tsanani a duniya ko a lahira.
Na farkonsu "Yi wa Allah shirka": Shi ne karkatar da kowanne nau'i daga Nau’ukan ibada ga wanin Allah, da daidaita wanin Allah da Allah cikin abin da ya keɓanci Allah a AllantakarSa da UbangidantakarSa da sunayenSa da siffofinSa.
Na biyunsu: "Saɓawa iyaye": Shi ne dukkanin abin da yake nuna cutarwa ga iyaye; magana ce ko aiki, da barin kyautata musu.
Na ukunsu "Kashe rai": ba tare da wani haƙƙi ba, kamar kisa a kan zalunci da ta'addanci.
Na huɗunsu "Rantsuwa mai dulmiyarwa": Ita ce rantsuwa alhali yana mai ƙarya yana sane cewa ƙarya yake, an ambaceta da hakan; domin cewa tana dulmiya mai yinta a laifi sannan a wuta.

Fassara: Turanci urdu Sifaniyanci Indonisiyanci Uighur Fassarar Bangaliyanci Fassara Yaren Faransanci Turkiyanci Rashanci Bosniyanci Sinhalese Kwafar laakwalwar zuwa bugere fassara Fassara da Yaren Chanise Farisanci Vietnam Tagalog Kurdawa Portuguese Malayalam Telgonci Swahili Yaran Tamili Yaran Barma Yaran Tailand Jamusanci Japananci bushtu Asami Albaniyanci السويدية الأمهرية الهولندية الغوجاراتية Kirgisisch النيبالية Yoruba الليتوانية الدرية الصربية الصومالية Kinyarwanda الرومانية المجرية التشيكية الموري Malagasy Italiyanci Oromo Kanadische Übersetzung الولوف Aserbaidschanisch الأوكرانية الجورجية
Manufofin Fassarorin

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Rantsuwa mai dulmiyarwa ba ta da kaffara; don tsananin haɗarinta da girmanta, kawai dai akwai [damar] tuba a cikinta.
  2. Taƙaituwa a kan ambaton waɗannan manyan laifukan guda huɗu a hadisin [ya kasance] don girman laifinsu ne, ba don su ne kadai ba.
  3. Zunubai sun kasu zuwa manya da ƙanana, babban laifi shi ne: Dukkanin zunubin da a cikinsa akwai uƙuba ta duniya, kamar haddi da tsinuwa, ko narko na lahira, kamar narko da shiga wuta, kuma manyan zunubai hawa-hawa ne wasu sun fi wasu muni a haramci.
  4. Kananan zunubai su ne waɗanda ba waɗannan ba.