1. Gida
  2. kashe kashe
  3. ILIMIN AƘIDA

Sabuntawa Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa

عَنْ عَائِشَةَ أُمِّ المؤمنين رضي الله عنها:
أَنَّ أُمَّ سَلَمَةَ ذَكَرَتْ لِرَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَنِيسَةً رَأَتْهَا بِأَرْضِ الْحَبَشَةِ، يُقَالُ لَهَا مَارِيَةُ، فَذَكَرَتْ لَهُ مَا رَأَتْ فِيهَا مِنَ الصُّوَرِ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «أُولَئِكَ قَوْمٌ إِذَا مَاتَ فِيهِمُ الْعَبْدُ الصَّالِحُ، أَوِ الرَّجُلُ الصَّالِحُ، بَنَوْا عَلَى قَبْرِهِ مَسْجِدًا، وَصَوَّرُوا فِيهِ تِلْكَ الصُّوَرَ، أُولَئِكَ شِرَارُ الْخَلْقِ عِنْدَ اللهِ».

Daga Nana Aisha Uwar Muminai - Allah ya yarda da ita -:
Cewa Ummu Salama ta gayawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta ga wata coci a kasar Habasha, ana kiranta Mariya, sai ta fadi duk abubuwan da ta gani a can na Hotuna, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Wadannan wasu mutane ne idan bawa na gari ya mutu daga cikinsu, ko kuma mutumin kirki, sai su gina masallaci akan kabarinsa, kuma su yi masa wadannan hotunan, wadannan su ne ashararen mutane a wajen Allah".

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Sahih Al-Bukhari - 434

Bayani

Uwar muminai Ummu Salama - Allah Ya yarda da ita - ta fadawa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa ta kasance a kasar Habasha ta ga wata coci - ana ce mata Mariya - a cikinta akwai hotuna da kawace- kawace da zane-zane; dan mamaki daga hakan! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana dalilan sanya wadannan hotunan; Sai ya ce: Wadannan wadanda kike fada sun kasance idan mutum nagari ya mutu a cikinsu, sai su gina masallaci akan kabarinsa suna sallah a cikinsa, su kuma zazzana wadancan hotunan, ya bayyana cewa mai aikata wancan shi ne mafi sharrin halitta a wurin Allah - Madaukakin sarki -; domin aikata shi yana kaiwa zuwa shirka da Allah - Madaukakin sarki -.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  1. Haramcin gina masallaci akan kabari, ko sallah a wurinsu, ko binne matattu a cikin masallaci; dan toshe kafa zuwa ga shirka.
  2. Gina masallaci akan kaburbura, da kafa hotuna a cikinsu, aikin yahudawa ne da kiristoci, kuma wanda ya aikata hakan, to hakika ya yi kamanceceniya da su.
  3. Haramcin rikon hotuna na masu rayuka.
  4. Wanda ya gina masallaci akan kabari ya kuma zana hotuna a cikinsa, to shi yana daga mafi sharrin halittar Allah - Madaukakin sarki -.
  5. Tsarewar da shari'a ta yi ga jinabin Tauhidi cikakkiyar tsarewa, ta hanyar toshe dukkanin hanyoyin da zasu kai zuwa ga shirka.
  6. Hani daga wuce gona da iri a salihai; domin cewa shi hanya ce ta fadawa cikin shirka.

Manufofin Fassarorin

60 Yare
EN English الإنجليزية
UR اردو الأوردية
ES Español الإسبانية
ID Indonesia الإندونيسية
UG ئۇيغۇرچە الأيغورية
BN বাংলা البنغالية
FR Français الفرنسية
TR Türkçe التركية
RU Русский الروسية
BS Bosanski البوسنية
SI සිංහල السنهالية
HI हिन्दी الهندية
ZH 中文 الصينية
FA فارسی الفارسية
VI Tiếng Việt الفيتنامية
TL Tagalog تجالوج
KU Kurdî الكردية
PT Português البرتغالية
ML മലയാളം المليالم
TE తెలుగు التلغو
SW Kiswahili السواحيلية
TA தமிழ் التاميلية
MY မြန်မာ البورمية
TH ไทย التايلندية
DE Deutsch الألمانية
JA 日本語 اليابانية
PS پښتو بشتو
AS অসমীয়া الأسامية
SQ Shqip الألبانية
SV Svenska السويدية
AM አማርኛ الأمهرية
NL Nederlands الهولندية
GU ગુજરાતી الغوجاراتية
KY Кыргызча القيرقيزية
NE नेपाली النيبالية
YO Yorùbá اليوروبا
LT Lietuvių الليتوانية
PRS دری الدرية
SR Српски الصربية
SO Soomaali الصومالية
TG тоҷикӣ الطاجيكية
RW Kinyarwanda الكينياروندا
RO Română الرومانية
HU Magyar المجرية
CS Čeština التشيكية
MOS Moore الموري
MG Malagasy المالاجاشية
OM Oromoo الأورومو
KN ಕನ್ನಡ الكانادا
WO Wolof الولوف
AZ Azərbaycan الأذربيجانية
UZ O‘zbek الأوزبكية
UK Українська الأوكرانية
KA ქართული الجورجية
MK Македонски المقدونية
KM ភាសាខ្មែរ الخميرية
BM Bambara البامبارية
PA ਪੰਜਾਬੀ البنجابية
MR मराठी الماراثية
KMR Kurmancî الكرمنجية