عَنْ عَائِشَةَ رضي الله عنها قَالَتْ:
قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللهِ، ابْنُ جُدْعَانَ كَانَ فِي الْجَاهِلِيَّةِ يَصِلُ الرَّحِمَ، وَيُطْعِمُ الْمِسْكِينَ، فَهَلْ ذَاكَ نَافِعُهُ؟ قَالَ: «لَا يَنْفَعُهُ، إِنَّهُ لَمْ يَقُلْ يَوْمًا: رَبِّ اغْفِرْ لِي خَطِيئَتِي يَوْمَ الدِّينِ».
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 214]
المزيــد ...
Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Na ce: Ya Manzon Allah, Ibn Jud'an ya kasance a lokacin jahiliyya yana sada zumunci, yana ciyar da miskinai, shin hakan zai anfanar da shi? Sai Ya ce: "Ba zai anfanar dashi ba, Lallai shi bai taba fada ba koda yini daya: Ya Ubangiji Ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako".
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 214]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari game da Abdullahi Ibnu Jud'an, ya kasance yana daga shugabannin Kuraishawa kafin Musulunci, Yana daga kyawawan ayyukansa cewa shi: Yana sada zumuncin 'yan uawansa, yana ciyar da miskinai, da wasunsu daga cikin mafifitan ayyukan da Musulunci ya kwadaitar akan aikatasu, da cewa wadannan ayyukan ba za su anfanar da shi a lahirarsa ba; saboda kafircewarsa ga Allah, kuma shi bai taba fada ba ko sau daya: Ya Ubangiji ka gafarta mini kuskurena ranar sakamako.