عَنْ أَبِي عَبْدِ الرَّحْمَنِ السُّلَمي رحمه الله قَالَ:
حَدَّثَنَا مَنْ كَانَ يُقْرِئُنَا مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّهُمْ كَانُوا يَقْتَرِئُونَ مِنْ رَسُولِ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَشْرَ آيَاتٍ، فَلَا يَأْخُذُونَ فِي الْعَشْرِ الْأُخْرَى حَتَّى يَعْلَمُوا مَا فِي هَذِهِ مِنَ الْعِلْمِ وَالْعَمَلِ، قَالُوا: فَعَلِمْنَا الْعِلْمَ وَالْعَمَلَ.
[حسن] - [رواه أحمد] - [مسند أحمد: 23482]
المزيــد ...
Daga Abu Abdurrahman Al-Sulami - Allah ya yi masa rahama - ya ce:
Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.
[Hasan ne] - [Ahmad ne ya rawaito shi] - [مسند أحمد - 23482]
Sahabbai - Allah Ya yarda da su - sun kasance suna koyo daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ayoyi goma daga Alkur’ani, ba sa cirata zuwa wasu har sai sun san abinda ke cikin wadannan goman na ilimi kuma suna aiki da shi, sai suka koyi ilimi da aiki gaba daya.