عن جابر رضي الله عنه:
أَنَّ رَجُلًا سَأَلَ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ، فَقَالَ: أَرَأَيْتَ إِذَا صَلَّيْتُ الصَّلَوَاتِ الْمَكْتُوبَاتِ، وَصُمْتُ رَمَضَانَ، وَأَحْلَلْتُ الْحَلَالَ، وَحَرَّمْتُ الْحَرَامَ، وَلَمْ أَزِدْ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا، أَأَدْخُلُ الْجَنَّةَ؟ قَالَ: «نَعَمْ»، قَالَ: وَاللهِ لَا أَزِيدُ عَلَى ذَلِكَ شَيْئًا.
[صحيح] - [رواه مسلم] - [صحيح مسلم: 15]
المزيــد ...
Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi -:
Lallai wani mutum ya tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Kana ganin idan na sallaci salloli wadanda aka wajabta, na azimci watan Ramdan, na halatta halal, na haramta haram, ban kara komai akan hakan ba, zan shiga Aljanna? Ya ce : "Eh", ya ce: Na rantse da Allah ba zan kara komai ba akan hakan ba.
[Ingantacce ne] - [Muslim ne ya rawaito shi] - [صحيح مسلم - 15]
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana cewa wanda ya sallaci salloli biyar, wadanda suka wajabta bai kara komai akan su ba na nafilifili, kuma ya azimci watan Ramadan bai yi tadawwa’i ba, ya kudirce halatta halal ya kuma aikata shi, ya kudirce haramta haram ya kuma nisanci ta, to shi zai shiga Aljanna.